Yanzu Yanzu: FG ba za ta biya kudin fansa don sakin daliban Kagara ba - Lai Mohammed

Yanzu Yanzu: FG ba za ta biya kudin fansa don sakin daliban Kagara ba - Lai Mohammed

- Kada wadanda suka yi garkuwa da yaran makarantar Kagara su yi tsammanin samun kudin fansa a cewar Lai Mohammed

- A cewarsa, masu aikata laifin suna aiki ne a kan tunanin mutane ta hanyar sace mata da kananan yara

- Ya kara da cewa gwamnati ba za ta bayyana dabarun ta na dawo da yaran ba

Gwamnatin tarayya ba za ta biya kudin fansa ba wajen neman sakin dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara da aka sace ba a cewar Lai Mohammed.

Channels TV ta rahoto cewa ya ce gwamnati za ta yi amfani da hanyoyi daban-daban don neman a saki daliban.

Ministan ya kuma nace cewa ba a biya fansa ba don sakin ‘yan makarantar Kankara da aka sace a jihar Katsina da kuma‘ yan matan makarantar Dapchi da ke jihar Yobe.

Yanzu Yanzu: FG ba za ta biya kudin fansa don sakin daliban Kagara ba - Lai Mohammed
Yanzu Yanzu: FG ba za ta biya kudin fansa don sakin daliban Kagara ba - Lai Mohammed Hoto: @FMICNigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata 13 a jihar Katsina

Ya ce:

"Muna amfani da dabaru daban-daban, ba ka watsi da gayyatar tattaunawa amma mutum kan boyewa zuciyarsa manyan dabarun da yake da su."

Da yake ci gaba da bayani, ya ce, “ Yan fashi a duk duniya suna aiki da ilimin halin mutane. Da gangan, suke dana tarkonsu a kan mata da yara saboda wannan shine abin da zai jawo hankalin duniya sosai. Wannan shine ainihin abin da yan fashi suke yi a duk duniya."

KU KARANTA KUMA: Fasto Adeboye yayi kira da a saki Leah Sharibu, ya ce "ba za mu saduda ba"

A gefe guda, wani babban dan bindiga a jihar Zamfara ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a saki malamai da daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara da aka sace a jihar Neja.

Dan fashin, Dogo Gide, wanda ke jar ragamar kula da dajin kudancin Zamfara ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da jami'an gwamnatin jihar Neja, jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, duk da cewa wadanda aka sacen ba su a sansaninsa, zai tattauna da sauran 'yan ta'addan don hanzarta sakinsu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel