Rashin tabbas yayin da lauya ya shigar da kara don hana majalisar dattawa tabbatar da sabon shugaban EFCC

Rashin tabbas yayin da lauya ya shigar da kara don hana majalisar dattawa tabbatar da sabon shugaban EFCC

- Abdulrasheed Bawa zai fuskanci shari'a dangane da nadin sa a matsayin shugaban EFCC

- Wani masanin shari'a, Osuagwu Ugochukwu, ya yi jayayya cewa akwai takaddama game da nadin Bawa

- Har yanzu Shugaban EFCC din bai yi martani ga matakin da kotu ta dauka ba

Yanzu haka ana shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan batun zabar Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC)

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa wani lauya, Osuagwu Ugochukwu, ya gabatar da karar da ke kalubalantar nadin Bawa don ya shugabanci hukumar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: FG ba za ta biya kudin fansa don sakin daliban Kagara ba - Lai Mohammed

Rashin tabbas yayin da lauya ya shigar da kara don hana majalisar dattawa tabbatar da sabon shugaban EFCC
Rashin tabbas yayin da lauya ya shigar da kara don hana majalisar dattawa tabbatar da sabon shugaban EFCC Hoto: Femi Adesina/Facebook, @DaminaboEric/Twitter
Asali: UGC

Lauyan ya nemi kotun da ta yanke hukunci kan ko Bawa ya cancanci a nada shi shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kuma bukaci kotu da ta yanke hukunci kan ko majalisar dattawa tana da hurumi a cikin doka don tabbatar da nadin Bawa, wanda ya yi ikirarin cewa ana ganin ya gaza da abin da ake bukata na sassan dokar da ta kafa EFCC.

Kotu ta ba majalisar dattawa da Bawa kwanaki 30 su tabbatar da dalilin da zai sa nadin ya dore.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an bawa majalisar dattawan Najeriya takardar kotu game da karar.

KU KARANTA KUMA: Ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka sace, in ji shugaban ‘yan fashin Zamfara

A gefe guda, lauya mai kare tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Tosin Ojaomo, ya ce ba ayi adalci a game da lamarin Ibrahim Magu da wasu abokan aikinsa ba.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa, Tosin Ojaomo, ya yi wannan magana ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Larabar nan.

Lauyan ya na magana ne a kan kwamitin binciken da shugaban kasa ya nada karkashin Ayo Salami domin a gano gaskiyar zargin da ke kan wuyan Magu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel