Ba ayi mani adalci ba, tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya fito ya na babatu
- Ibrahim Magu ya na kukan ba ayi masa adalci a binciken da aka yi a EFCC ba
- Wani Lauyan tsohon shugaban na EFCC, Tosin Ojaomo ne ya yi magana a yau
- Tosin Ojaomo ya ce ba ayi wa Magu da sauran Jami’an da aka bincika adalci ba
Lauya mai kare tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Tosin Ojaomo, ya ce ba ayi adalci a game da lamarin Ibrahim Magu da wasu abokan aikinsa ba.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa, Tosin Ojaomo, ya yi wannan magana ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Larabar nan.
Mista Ojaomo yake cewa: “Kwatsam sai ga rahoto ya fito, an yi wani sabon nadin mukami… gaskiya ba ayi wa Magu adalci a kan lamarin nan ba.”
“Mu na magana ne a kan darajar mutum a idon jama’a, da irin bata masa suna da aka yi a waje.”
KU KARANTA: An ba Gwamnati damar yin gwanjo da dukiyar Jimoh Ibrahim
Lauyan ya na magana ne a kan kwamitin binciken da shugaban kasa ya nada karkashin Ayo Salami domin a gano gaskiyar zargin da ke kan wuyan Magu.
Masanin shari’ar yake cewa bayan Ibrahim Magu, an dakatar da sauran wasu jami’an EFCC a sakamakon binciken da kwamitin Ayo Salami ya gudanar.
Bayan an kammala wannan aiki, Ojaomo ya ce yanzu kamar ba ta wadannan jami’ai ake yi ba.
“Ba maganar Magu ba ce kawai, akwai mutane a hukumar da aka dakatar, duka wadannan mutane kallon mutuncin da ake yi masu ya na fuskantar barazana.”
KU KARANTA: Shugaba kasa Buhari ya nada sabon Shugaban EFCC
Ojaomo ya so ace an fito an yi bayanin abin da kwamitin binciken da aka kafa su ka gano, domin a wanke Magu, ko kuma a tabbatar da duk zargin da ke kansa.
A jiya ne hukumar EFCC ta yi raddi a kan masu zargin sabon Shugabanta, Abdulrasheed Bawa da laifin gwanjon wasu kayan sata a lokacin ya na rike da ofis a Ribas.
EFCC ta wanke Abdulrasheed Bawa, ta ce babu wata badakala da ke wuyan sabon shugaban na ta.
Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce sam babu hannun sabon shugaban a badakalar yin gwanjo da manyan motoci da aka yi a 2019.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng