Makiyaya basu bukatar izininka don zama a dajika, Gwamnan Bauchi ga Akeredolu

Makiyaya basu bukatar izininka don zama a dajika, Gwamnan Bauchi ga Akeredolu

- Kauran Bauchi, sanata Bala Mohammed ya ce makiyaya basu bukatar izinin takwaransa na Ondo don zama a dajikan kudanci

- Gwamnan ya ce kowanne dan Najeriya yana da damar zama a kowacce jiha cikin kasar nan kamar yadda kundin tsarin mulki yace

- Gwamnan ya tabbatar da cewa kasa ta gwamnatocin jihohi da tarayya ce kuma dan Najeriya zai zauna inda yake so

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a jiya ya ce 'yan kasa basu bukatar izinin takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, domin zama a dajikan jihohin kudu masu yamma.

Gwamnan jihar Bauchi wanda yayi jawabi a wani shirin gidan talabijin, a bayyane yake magana ga Akeredolu wanda ya bukaci makiyaya su bar dajikan.

Gwamnan ya kara da cewa 'yan Najeriya basu bukatar izinin kowanne gwamna idan za su yada zango a kowacce jiha a cikin kasar nan, ThisDay ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: Saraki da jiga-jigan PDP sun yi ganawar sirri da IBB, Abdulsalami

Makiyaya basu bukatar izininka don zama a dajika, Gwamnan Bauchi ga Akeredolu
Makiyaya basu bukatar izininka don zama a dajika, Gwamnan Bauchi ga Akeredolu. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

Umarnin da Akeredolu ya bada ya janyo cece-kuce inda fadar shugaban kasa da wasu gwamnoni da suka hada da Mohammed ke cewa bashi da damar bai wa makiyayan umarnin tattara komatsansu su bar jihar.

A jiya, Gwamna Mohammed ya ce: "Kasa a hannun gwamnatocin jihohi da tarayya take amma dan Najeriya baya bukatar izinin wani gwamna ko gwamnatin tarayya don zama a ko ina.

"Baku bukatar izinin gwamnan Bauchi ko gwamnan Ondo wurin zama a dajika. A karkashin sashi na 41 na kundin tsarin mulki kowa yana da damar zama a ko ina."

Gwamnan jihar Ondo ya caccaki Mohammed a kan cewa da yayi makiyaya na da ikon yawo da bindiga kirar AK47 domin bai wa kansu kariya.

KU KARANTA: Da duminsa: Rikicin sarauta yasa an maka dokar kulle a Gombe

A wani labari na daban, Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban PRTT yace zai iya rasa kafarsa indai ba a bashi damar zuwa asibiti neman magani ba, The Cable ta wallafa.

Dama Maina yana hannun hukuma akan zargin wawurar naira biliyan biyu na kudin fansho kuma ya tsere ya bar sanata mai wakiiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, a hannun hukuma bayan ya tsaya masa a matsayin tsayayye.

An samu nasarar damkarsa a jamhuriyar Nijar inda ya lallaba ya shige, a ranar 3 ga watan Disamban 2020.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng