Zan iya rasa kafata idan aka hana ni beli, Maina ya sanar da kotu

Zan iya rasa kafata idan aka hana ni beli, Maina ya sanar da kotu

- Tsohon shugaban PRTT, Abdulrasheed Maina, ya ce zai iya rasa kafarsa idan ba a bayar da belinsa ya nemi magani ba

- Maina yana gidan gyaran hali ne bisa zargin wawurar kudaden fansho na N2,000,000,000, kuma ya tsere ya daina bayyana a kotu

- Maina ya bar Sanata Ali Ndume a hannun hukuma a watan Satumba, wanda ya tsaya masa a matsayin tsayayye

Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban PRTT yace zai iya rasa kafarsa indai ba a bashi damar zuwa asibiti neman magani ba, The Cable ta wallafa.

Dama Maina yana hannun hukuma akan zargin wawurar naira biliyan biyu na kudin fansho kuma ya tsere ya bar sanata mai wakiiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, a hannun hukuma bayan ya tsaya masa a matsayin tsayayye.

An samu nasarar damkarsa a jamhuriyar Nijar inda ya lallaba ya shige, a ranar 3 ga watan Disamban 2020.

KU KARANTA: Kwamishina a Zamfara yayi murabus, ya ce APC za ta kwace kujerar Matawalle

Zan iya rasa kafata idan aka hana ni beli, Maina ya sanar da kotu
Zan iya rasa kafata idan aka hana ni beli, Maina ya sanar da kotu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Sannan an dakatar da bayar da belin Maina inda aka sa ya cigaba da zama a gidan gyaran hali har sai an kammala shari'arsa.

A zaman kotu da aka yi ranar Juma'a, lauyan Maina, Sani Katu ya bukaci a bayar da belin Maina saboda halin rashin lafiyar da yake ciki.

A takardar kotu Katu ya ce Maina zai iya rasa kafarsa matukar ba a bashi beli ya nemi lafiya ba.

"Muna bukatar alkali ya taimaka ya bayar da belin Maina sakamakon hali na rashin lafiya da yake ciki, don hakan babban hatsari ne ga rayuwarsa."

Saidai Alkalin, Mohammed Abubakar, lauyan EFCC ta nuna rashin amincewarsa akan belin.

"Idan aka duba yadda aka bashi beli a karo na farko kuma ya bayar da kunya, ba abin amincewa bane," a cewar Abubakar.

"Maina yana son nuna cewa likitocin Najeriya basu da kayan aiki da kwarewar da zasu iya kulawa da lafiyarsa. Tabbas akwai kwararrun likitoci a gidan gyara hali."

Alkali Okon Abang, ya dakatar da neman belin har sai ranar 25 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA: Kar ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Minista ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, bai wuce kwana 2 ba da 'yan Boko Haram suka afka Egiri, Zira I da II dake karkashin karamar hukumar Biu wanda hakan yayi sanadiyyar asarar gidaje da dama, sun kara kai hari kananun hukumomin Marte da Gubio dake jihar Borno a daren Talata.

Kamar yadda labarai suka gabata, 'yan bindigan sun afka mazaunin 'yan sa kai da mahauta inda suka bude musu wuta har suna kashe wasu suka kuma ji wa wasu raunuka kafin sojoji su mayar musu da harin.

A Marte kuwa sai da 'yan bindigan suka afka anguwar sabuwar Marte da miyagun makamai suna harbe-harbe jama'a na gudun neman tsira.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel