Da duminsa: Saraki da jiga-jigan PDP sun yi ganawar sirri da IBB, Abdulsalami
- Shugabannin PDP sun yi taron sirri tare da dattawan Najeriya
- An yi taro tsakanin Ibrahim Babangida da Abdulsalami a ranar Juma'a
- Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa ya bayyana makasudin taron a Twitter
A kokarin dinke baraka kafin zuwan zaben 2023, shugabannin jam'iyyar PDP a ranar Juma'a 19 ga watan Fabrairu sun samu ganawa da tsohon shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Babangida.
Bakin sun samu shugabancin tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, wadanda suka hallara a katafaren gidan tsohon shugaban kasan da ke Hilltop a Minna.
Hakan yana zuwa ne bayan kwanaki biyar da kwamitin sasancin suka kai wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kai hari kananan hukumomi 2 a Borno, sun sheke mutane
A cikin kwanakin nan, jam'iyyar PDP na cike da rikicin shugabanci wanda ya janyo suka rasa manyan jiga-jigansu.
Wadanda suka sauya sheka cikin kwanakin nan sun hada da Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da kuma tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel.
Kwamitin da ya samu shugabancin Saraki ya samu ganawa da AbdulSalami Abubakar. A yayin bayani a kan makasudin ziyarar, Saraki ya yi wallafa a shafinsa na Twitter.
KU KARANTA: Fani-Kayode ya caccaki Saraki a kan ziyarar da ya kaiwa Jonathan
A wani labari na daban, kwamishinan aikin hajji, Alhaji Sirajo Maikatako, ya yi murabus. Ya bayyana hakan ne a wani taron 'yan jam'iyyar APC da aka yi a Gusau ranar Alhamis, Daily Trust ta wallafa.
Ya bayyana yakininsa inda yace jam'iyyar APC ce za ta lashe kaf kujerun jihar a zaben 2023, har yana cewa ya yi aiki ne karkashin jam'iyyar PDP a matsayin shugaba ba dan siyasa ba.
"Ina farin cikin sanar da canja shekata daga shugabanci a karkashin jam'iyyar PDP. Na yi hakan ne don nuna matukar goyon baya ga shugabana a harkar siyasa, Sanata Kabiru Marafa don samun wanzuwar kwanciyar hankali da hadin kan jam'iyyar APC."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng