Da duminsa: Rikicin sarauta yasa an maka dokar kulle a Gombe

Da duminsa: Rikicin sarauta yasa an maka dokar kulle a Gombe

- Gwamnatin jihar Gombe sun sanya kullen sa'o'i 24 sakamakon dakatar da babban titin Yola zuwa Gombe a ranar Juma'a

- Hakan ya biyo bayan dakatar da yawo a karamar hukumar Billiri dake jihar akan babbar kujerar sarauta ta Mai Tangale

- Daruruwan matan garin sun taru a titina suna ganin kamar da gangan gwamnatin Yahaya tayi don ta zabi wanda ta ga dama

A ranar Juma'a, gwamnatin jihar Gombe ta sanya kullen sa'o'i 24 sakamakon dakatar da titin Yola zuwa Gombe wanda yake hana isa karamar hukumar Billiri dake cikin jihar, saboda babbar kujerar sarauta ta Mai Tangale.

Daruruwan mata sun taru a wurare suna zargin da gangar gwamnatin Yahaya tayi hakan saboda ta zabi duk wanda ta ga dama ba wai zabin jama'a ba, The Punch ta wallafa.

Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin kullen bayan wani kwarya-kwaryan taro da tayi da sakataren jihar, Farfesa Ibrahim Njodi, saboda hakan ne zai samar da zaman lafiya a yankin.

KU KARANTA: Kwamishina a Zamfara yayi murabus, ya ce APC za ta kwace kujerar Matawalle

Da duminsa: An saka dokar kulle a karamar hukumar Billiri ta Gombe
Da duminsa: An saka dokar kulle a karamar hukumar Billiri ta Gombe. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar ta tabbatar da yadda zata samar da cikakken zaman lafiya.

A cewar Njodi, "Bayan ganin yadda rikici da tashin hankali ya fara aukuwa a garin Billiri, wanda yayi cikas da zaman lafiya, rayuka da dukiyoyin jama'a, gwamnatin jihar Gombe ta sanya kullen sa'o'i 24 a karamar hukumar Billiri tun daga 6:00 pm na yau, 19 ga watan Fabrairun 2021.

"Gwamnati tana so ta tabbatar da zaman lafiya tsakanin 'yan jihar da kuma kulawa da lafiya da rayukan jama'a. Don haka gwamnati ta dakatar da duk wani taron jama'a a karamar hukumar Billiri.

"Don haka ana umartar duk wasu jami'an tsaro da su tabbatar da dokar. Ana umartar duk wasu 'yan jihar da su kiyaye doka don samun zaman lafiya"

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kai hari kananan hukumomi 2 a Borno, sun sheke mutane

A wani labari na daban, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya ce hakkin kowanne dan kasa ne ya kasance a ankare da rashin tsaron Najeriya.

Magashi ya sanar da hakan ne yayin wata hira da yayi da manema labarai kuma AIT ta nada tare da wallafawa a shafinta na Twitter. Ya ce su nuna cewa su ba sakarkaru bane ta hanyar bai wa kansu kariya.

Ya ce sau da yawa 'yan bindiga na aiki ne da harsasai kadan domin saka tsoro a zukatan jama'a, Vanguard ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: