COVID-19: Daga bisani, El-Rufai ya amince a bude dukkan makarantu

COVID-19: Daga bisani, El-Rufai ya amince a bude dukkan makarantu

- Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da ranar Litinin 22 ga watan Fabrairu a matsayin ranar komawa makarantu a jihar

- Kamar yadda gwamnatin ta amince, gaba daya azuzuwan da basu koma ba suna iya komawa, na makarantun gwamnati da na kudi

- Kwamishinan ilimi, Dr Shehu Muhammad ne ya bayyana hakan ranar Juma'a ta wata takarda, inda yace har makarantun islamiyyoyi zasu iya komawa

Gwamnatin jihar Kaduna ra amince da ranar Litinin 22 ga watan Fabrairun 2021 a matsayin bangare na biyu na komawa makarantu a fadin jihar, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda gwamnatin ta amince, duk azuzuwan SS2, SS1 da kuma JS2 na makarantun gwamnati da na kudi da kuma azuzuwan firamare na 4, 5 da 6 a makarantun gwamnati da kuma azuzuwan firamare 3, 2, 1 da kuma duka azuzuwan Nursery na makarantun kudi da kuma islamiyya duk su bude.

Kwamishinan ilimi na jihar, Dr Shehu Muhammad, ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma'a.

KU KARANTA: Zan iya rasa kafata idan aka hana ni beli, Maina ya sanar da kotu

COVID-19: Daga bisani, El-Rufai ya amince a bude dukkan makarantu
COVID-19: Daga bisani, El-Rufai ya amince a bude dukkan makarantu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A cewarsa, ma'aikatar ilimi ta baiwa duk wasu shugabannin makarantu na firamare da sakandare umarnin bude makarantun kwana da na jeka-ka-dawo a ranar Litinin, 22 ga watan Fabrairun 2021.

A cewarsa, hukumar kulawa da COVID-19 ta jihar za ta cigaba da lura da makarantu idan suna kulawa da bin dokokin hana yaduwa daga cutar don samun damar yin karatu cikin koshin lafiya.

"Ana bai wa shugabannin makarantun gwamnati da na kudi da su kula da dokokin kare kai daga cutar COVID-19 don kin bin dokar zata iya janyo rufe makarantar ba tare da sanarwa ba," yace.

KU KARANTA: A bar 'yan Najeriya su dinga yawo da makamai idan makiyaya suna yi, Fani-Kayode

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Yerima ya kaiwa Haruna Maiyasin Katsina, sarkin Shasha, jihar Oyo, ziyara bisa rikici da tashin hankalin da ya faru a jihar.

Yerima ya tattauna da wadanda lamarin ya faru dasu kuma ya yi kira akan zaman lafiya a yankin.

Ya hori mazauna yankin da su zauna lafiya da junansu kuma su hada kawunansu, The Cable ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng