A bar 'yan Najeriya su dinga yawo da makamai idan makiyaya suna yi, Fani-Kayode
- Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya bukaci gwamnati ya bai wa jama'a damar yawo da makamai
- Jigon jam'iyyar PDP din ya ce in dai makiyaya na da damar yawo da AK47 toh dole ne jama'a su dinga yawo da makamai
- Ya ce da gwamnati ta sauke hakkinta na kula da rayukan jama'a, zakakurai kamar Sunday Igboho ba za su bayyana ba
Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode ya sanar da gwamnatin tarayya da ta bar 'yan Najeriya su dinga daukar makamai idan har ta bar Fulani suna yawo da AK47 domin kare kansu da shanunsu.
Kamar yadda yace, idan aka duba lamarin ta haka toh dole ne a baiwa jama'a damar yawo da makamai domin bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga da kuma makiyayan, Vanguard ta ruwaito.
Ya ce hanyar da ta fi dacewa wurin shawo kan matsalar tsaron kasar nan shine dukkan matakai na gwamnati su hada karfi da karfe kuma a hana 'yan Najeriya yawo da makamai.
KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya gwangwaje 'yan kasuwar Shasha da N18.5m na rage radadi
Ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin ziyarar ban girma ga Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho a gidansa da ke Soka, Ibadan.
Fani-Kayode wanda yayi taron sirri da Sunday Igboho na fiye da sa'o'i uku ya ce idan da ace gwamnati ta karba tare da sauke nauyinta na bai wa rayukan 'yan Najeriya kariya, jaruman mutane kamar Sunday Igboho ba za su bayyana ba.
KU KARANTA: Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri
A wani labari na daban, tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayi kira ga gwamnati da ta saka tsauraran dokoki da za su daidaita hauhawar yawan jama'a a kasar nan.
Sanusi wanda yayi magana a ranar Laraba yayin wani taro a Legas, ya ce ya dace jama'a su dinga haifar yaran da za su iya kula da su, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace, abubuwan da ke bayyana a halin yanzu sun nuna cewa gwamnati ba za ta iya samar da dukkan ababen more rayuwa da ake bukata ba.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng