Mu 'yan uwan juna ne, Tsohon gwamnan Zamfara ya ziyarci Shasha

Mu 'yan uwan juna ne, Tsohon gwamnan Zamfara ya ziyarci Shasha

- Ahmed Yerima, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya kaiwa Haruna Maiyasin Katsina, Sarkin Shasha, jihar Oyo ziyara akan rikicin jihar

- Yerima ya tattauna da wadanda lamarin ya shafa kuma yayi kira akan zaman lafiyar mazauna yankin

- Ya hori mazauna jihar da su hada kawunansu a matsayin 'yan uwan juna kuma su cigaba da zama lafiya da juna

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Yerima ya kaiwa Haruna Maiyasin Katsina, sarkin Shasha, jihar Oyo, ziyara bisa rikici da tashin hankalin da ya faru a jihar.

Yerima ya tattauna da wadanda lamarin ya faru dasu kuma ya yi kira akan zaman lafiya a yankin.

Ya hori mazauna yankin da su zauna lafiya da junansu kuma su hada kawunansu, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Sanusi ya bukaci gwamnati ta kayyadewa 'yan Najeriya yawan iyalin da za su haifa

Mu 'yan uwan juna ne, Tsohon gwamnan Zamfara ya ziyarci Shasha
Mu 'yan uwan juna ne, Tsohon gwamnan Zamfara ya ziyarci Shasha. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Yayin da yake tattaunawa dasu, ya shawarcesu da su manta lamarin da ya faru tsakaninsu, tsohon gwamnan ya yi kira ga Katsina da ya dawo da jama'arsa don su cigaba da kasuwanci ba yare da tsoro ba.

Yerima ya kwatanta mutanen jihar Oyo a matsayin mutane masu nuna kauna da so kuma masu kawar da bambance-bambance na addini ko kabilanci.

Katsina ya mika godiyarsa ga Yerima saboda zumuncinsa da kuma samun lokacin kai wa mutanen Shasha ziyara.

"Duk an taru an zama daya, mun auri junanmu, auratayya ta shiga tsakanin hausawanmu da 'yan kabilar ibo a Shasha, amma duk 'yan Najeriya ne mu," a cewarsa.

KU KARANTA: Kar ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Minista ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, bai wuce kwana 2 ba da 'yan Boko Haram suka afka Egiri, Zira I da II dake karkashin karamar hukumar Biu wanda hakan yayi sanadiyyar asarar gidaje da dama, sun kara kai hari kananun hukumomin Marte da Gubio dake jihar Borno a daren Talata.

Kamar yadda labarai suka gabata, 'yan bindigan sun afka mazaunin 'yan sa kai da mahauta inda suka bude musu wuta har suna kashe wasu suka kuma ji wa wasu raunuka kafin sojoji su mayar musu da harin.

A Marte kuwa sai da 'yan bindigan suka afka anguwar sabuwar Marte da miyagun makamai suna harbe-harbe jama'a na gudun neman tsira.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel