Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa

Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa

- Wani matashi ya tsere ya bar gari tare da surukarsa bayan matarsa ta haifa masa da

- Matashin, Ryan, ya shaku da surukarsa ne sakamakon zaman da suka yi a lokacin kulle

- Bayan budurwarsa, Jesse Aldridge ta haihuwa, sai Ryan ta fada mata baya son cigaba da soyayyar

- Jim kadan bayan hakan Ryan da surukarsa suka sauya gida suke tsere wani gari mai nisa da inda Aldridge ta ke

Wani matashi mai suna Ryan Shelton wanda keda shekaru 29, ya wanke kafa ya gudu ya bar gari tare da mahaifiyar budurwarsa bayan budurwar ta sa ta haifa ma sa jinjirin, The Nation ta ruwaito.

Budurwar ta sa Jesse Aldridge, mai shekaru 24, its ce ta bayyanawa jaridar The Sun mamakinta na faruwar wannan lamari.

Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa
Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Jesse ta bayyana cewar saurayin na ta ya ci amanarta a yayin da take da tsohon ciki lokacin su na zaune tare da mahaifiyarta da mijinta mai suna Eric.

DUBA WANNAN: Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger

Ta kuma ce lamarin ya samo asali ne sadda su ka tare a gidan mahaifiyarta, a yayin da mahaifiyarta ta fara caka-caka da Ryan.

Kawai ranar da ta dawo gida da santalelen jinjiri, sai ta tarar da sun gudu tare sun koma wani gidan wanda nisan sa ya kai mil 30.

Jesse ta ce "mun kasance cikin zaman kulle a gida na tsawon lokaci wanda ban ji dadin zaman ba sakamakon yadda saurayina da mahaifiyata su ke yawan wasan banza. Kamata ya yi ace ta so jikokinta ta kuma nuna ma su kulawa ba wai ta je ta na wasanni da saurayina ba."

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Ƴan Nigeria ba su buƙatar izini kafin su zauna a dazukan Ondo

Rahoto ya nuna cewar Ryan ya yanke alakarsu ne bayan ta haifa ma sa jinjirin a inda ya bayyana ma ta cewar shi ba zai iya cigaba da soyayya da ita ba. Ita kuwa mahaifiyarta cewa ta yi "dan adam ba shi da ikon hana ran sa abun da ya ke so"

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164