Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya naɗa sabbin shugabanni a NSCDC da NCoS

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya naɗa sabbin shugabanni a NSCDC da NCoS

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabin shugabanni a hukumomoin NSCDC da NCos

- An nada Ahmed Abubakar Audi a matsayin sabon shugaban NSCDC yayin da ya zabi Halliru Nababa ya jagoranci NCoS

- Sanarwar nadinsu ya fito ne ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida, Mohammed Manga, ta shafin Twitter na ma'aikatar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Ahmed Abubakar Audi a matsayin sabon babban kwamandan hukumar tsaro da NSCDC da aka fi sani da Civil Defence.

Nadin na zuwa ne bayan murabus din da tsohon shugaban hukumar ta NSCDC, Abdullahi Gana Muhammadu ya yi.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban NSCDC
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban NSCDC. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Mohammed Manga ne ya sanar da nadin cikin wata wallafa da ya yi ta hanyar amfani da shafin Twitter na ma'aikatar.

DUBA WANNAN: Hotunan ɗalibar da ta tafi makaranta da bindiga za ta harbi malamin da ya ce ta aske gashinta mai launi

Sanarwar ta ce, "Ahmed Audi ya zama zakara cikin wadanda aka yi wa gwaji domin tabbatar da tsarin adalci da @MinOfInteriorNG ta hannun kwamitin ta domin tabbatar da cewa wanda ya fi dacewa cikin jami'ai masu babban mukami ne ya maye gurbin shugaba mai barin garo.

KU KARANTA: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

Kazalika, Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Haliru Nababa mni a matsayin sabon shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali @CorrectionsNg inda ya ke jiran amincewar majalisar dattawa kamar yadda dokar ta tanada.

Ministan Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola ya taya wadanda aka yi wa nadin murna ya kuma yi kira gare su da su hada kai da sauran hukumomin tsaro domin bada tsaro da yan kasa da kula alaka mai kyau da baki kamar yadda ya ke a tsarin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel