Da duminsa: NEC ta nemi jihohi da su biya diyya ga wadanda rikicin makiyaya da manona ya rutsa dasu

Da duminsa: NEC ta nemi jihohi da su biya diyya ga wadanda rikicin makiyaya da manona ya rutsa dasu

- Majalisar tattalin arziki ta nemi gwamnoni su biya jama'ar da rikici ya rutsa dasu diyya

- Hukumar tana bukatar a biya wadanda rikicin makiyaya da manoma ya shafa ne a jihohi

- Hakazalika hukumar ta lura cewa mutane da yawa sun yi asarar dukiya sakamakon rikicin

Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) a ranar Alhamis ta amince gwamnatocin jihohi su biya diyya ga wadanda rikicin manoma da makiyaya ya shafa, wadanda suka rasa abin yi.

Majalisar, wacce Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ta kuma karfafawa jihohi gwiwa don inganta zamanantar da kiwon dabbobi.

Wadannan sune shawarwari guda biyu da aka cimma yayin taron a Old Banquet Hall na fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Rashin nuna kwarewar jami'an tsaro ke jawo sace dalibai, in ji Solomon Dalong

Da dumi-dumi: NEC ta nemi Jihohi da su biya diyya ga makiyaya da manona da rikici ya rutsa dasu
Da dumi-dumi: NEC ta nemi Jihohi da su biya diyya ga makiyaya da manona da rikici ya rutsa dasu Hoto: THISDAYLIVE
Source: UGC

Da yake magana a kan batun a taron bayan majalisar, Gwamnan Ogun Dapo Abiodun ya lura cewa mutane da yawa sun yi asara a hare-haren da aka yi kuma dole ne a sanya su cikin yanayin biyan diyya.

An ruwaito ya ce majalisar ta sake sadaukar da kai ga kare dukkan mazauna ba tare da nuna banbanci ba, ya kara da cewa Gwamnoni za su kuma tabbatar da cewa an kamo masu laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu.

KU KARANTA: Tsoron sace dalibai: Gwamnatin jihar Osun ta garkame makaranta

A wani labarin, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnoni hudu daga yankin arewacin Najeriya a yanzu haka suna ganawa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabanin Fulani, manoma da sarakunan gargajiya a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel