Kar ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Minista ga 'yan Najeriya

Kar ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Minista ga 'yan Najeriya

- Ministan tsaro na kasar nan, ya bukaci 'yan Najeriya da su dinga bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga

- Ya ce kada jama'a su nuna sakarcinsu a fili domin kuwa 'yan bindigan da harsasai kalilan suke kai hari

- Ya kara da cewa a zamaninsu suna tunkarar manyan cutarwa balle wannan 'yan kananan da ba za su gagara ba

Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya ce hakkin kowanne dan kasa ne ya kasance a ankare da rashin tsaron Najeriya.

Magashi ya sanar da hakan ne yayin wata hira da yayi da manema labarai kuma AIT ta nada tare da wallafawa a shafinta na Twitter.

Ya ce su nuna cewa su ba sakarkaru bane ta hanyar bai wa kansu kariya. Ya ce sau da yawa 'yan bindiga na aiki ne da harsasai kadan domin saka tsoro a zukatan jama'a, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya gwangwaje 'yan kasuwar Shasha da N18.5m na rage radadi

Kada ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Ministan tsaro
Kada ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Ministan tsaro. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yara 7 sun samu rauni bayan 'abu mai fashewa' ya tarwatse suna wasa dashi a Kaduna

A kalamansa, "Hakkin kowa ne ya kasance a ankare kuma ya nemi kariya a lokacin da ya dace. Kada mu kasance sakarkaru.

"Sau da yawa 'yan bindiga na zuwa ne da harsasai kalilan sannan su yi ta harbe-harbe don kowa ya tsorata.

"A zamanin muna yarinta, mun tsayuwa tsayin daka wurin yakar duk wata cutarwar da ta tunkaro mu. Ban san me yasa jama'a ke gudun wannan karamar ba.

"Ku tsaya tsayin daka kuma su bayyana cewa kauyawan nan da ke hararsu za su iya kare kansu.

"Hakkinmu ne mu tabbatar da cewa ba a cutar da 'yan Najeriya ba kuma muna iya kare nagartar kasar nan. Za mu iya hakan komai tsanani."

A wani labari na daban, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC ba a zaben shugaban kasa 2023.

Saraki ya bayyana hakan a ranar Talata bayan ya tasa 'yan kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP zuwa gidan tsohon shugaban kasar dake Abuja.

A taron da suka yi da Jonathan an samu labarai iri-iri na batun shugabannin jam'iyyar APC da tsohon shugaban kasar wanda ya janyo cece-kuce iri-iri a kafafen sada zumuntar zamani, inda har wasu suke zaton APC za ta tsayar da Jonathan takara a 2023.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel