2023: Jonathan ba zai saki kansa ba da har APC za ta kwacewa PDP, Bukola Saraki

2023: Jonathan ba zai saki kansa ba da har APC za ta kwacewa PDP, Bukola Saraki

- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce batun tsayawar Goodluck Jonathan takara a jam'iyyar APC maganar kanzon kurege ce

- Saraki ya bayyana hakan ne bayan sun yi wani taro da Jonathan akan cece-kucen da suka fara yawaita akan shugabannin APC da shi

- Duk da yadda Jonathan da jiga-jigan jam'iyyar APC suke taro akai-akai, amma tsohon shugaban kasan yana cigaba da tsayawa tsayin-daka da cewa yana nan a PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC ba a zaben shugaban kasa 2023.

Saraki ya bayyana hakan a ranar Talata bayan ya tasa 'yan kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP zuwa gidan tsohon shugaban kasar dake Abuja.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ku yi addu'a Ubangiji ya kawowa Najeriya sauki, Sarkin Bauchi

2023: Jonathan ba zai saki kansa ba da har APC za ta kwacewa PDP, Bukola Saraki
2023: Jonathan ba zai saki kansa ba da har APC za ta kwacewa PDP, Bukola Saraki. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

A taron da suka yi da Jonathan an samu labarai iri-iri na batun shugabannin jam'iyyar APC da tsohon shugaban kasar wanda ya janyo cece-kuce iri-iri a kafafen sada zumuntar zamani, inda har wasu suke zaton APC za ta tsayar da Jonathan takara a 2023.

Duk da Jonathan da shugabannin APC suna yawan yin taro a cikin kwanakin nan, ya cigaba da tabbatar wa da kowa cewa ba gaskiya bane batun canja shekarsa har da tsayawa takara.

Sai dai Saraki ya sanar da manema labarai cewa mutane ne kawai suke yada labaran kanzon kurege, amma Jonathan na nan a jam'iyyarsa ta PDP.

KU KARANTA: 'Yan bindiga na tara kudin siyan makami mai linzami na harbo jiragen sama, Gumi

A wani labari na daban, wani sojan sama na Najeriya ya rasu sakamakon artabu da 'yan bindiga a jihar Kaduna.

Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani, ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter. Ya sanar da yadda 'yan bindigan suka kashe Abubakar Muhammad Ahmad tare da wasu abokan aikinsa a babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Sani ya bayyana cewa sojan na shirye-shiryen aurensa a makonni uku masu zuwa. Ya ce ya yi ta'aziyyar marigayin sojan a gidansu da ke Kaduna a ranar Lahadi, 14 ga watan Fabrairun 2014.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng