Ba mu da takamanman dan takarar shugaban kasa har yanzu, in ji PDP

Ba mu da takamanman dan takarar shugaban kasa har yanzu, in ji PDP

- Jam'iyyar PDP ta karya jita-jitan zawarcin dan takarar shugaban kasa ko wanene shi

- Jam'iyyar tace ba ta shirya fara siyar da fom ba balle ta yanke wanda za a ba tikitin takarar

- Hakazalika ta bayyana bata goyon bayan ko wane dan takara sai dai demokradiyya zalla

Jam'iyyar Peoples Democractic Party (PDP) a Najeriya ta karyata zantukan da ke ta yawo a kafafen sada zumunta da cewa tana zawarcin dawo da tsohon dan takarar ta na shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin mai tsayawa a zaben 2023.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiya, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambaya kan shirin jam’iyyar na jawo Atiku don bashi tikitin, a yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, ranar Laraba.

KU KARANTA: Bana son annobar Covid-19 ta kare, saboda a lokacinta na sayi jirgi na 3, in ji Fasto

Ba mu da taka-mai-man dan takarar shugaban kasa har yanzu, in ji PDP
Ba mu da taka-mai-man dan takarar shugaban kasa har yanzu, in ji PDP Hoto: The Sun News
Asali: UGC

Kola ya ce a matsayinsu na jam’iyya, PDP a shirye take ko yaushe don kare dimokiradiyya, kuma ba za ta yadda ta goyi bayan dan takara ko wanene shi ba.

"Ba mu fara sayar da fom ba, har sai lokacin, ba mu san wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar a shekarar 2023. Bugu da ƙari, ba mu fara sayar da fom ba," in ji shi.

A wata tattaunawa ta musamman da Daily Trust, wani memba na kwamitin amintattu (BoT) kuma tsohon ministan harkokin ’yan sanda, Adamu Maina Waziri, ya ce akwai fahimtar juna tsakanin jiga-jigan jam’iyyar don rike tikitin takarar shugaban kasa a Arewa.

KU KARANTA: Babu hujjar kimiyya mai nuna ganyen Bay da Kanunfari na maganin ciwon gabbai

A wani labarin, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta nuna damuwarta kan rikicin kabilanci a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, wanda ya kai ga rasa rayukan mutane da dama, Vanguard News ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rashin fahimta tsakanin kabilun biyu daban-daban a kasuwar Shasa da ke karamar Hukumar Akinyele a Ibadan ta haifar da rikici na kabilanci wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel