Budurwa ta kalubalanci mutane da su shiga gasar rubutu mai kyau, ta wallafa hoton littafinta

Budurwa ta kalubalanci mutane da su shiga gasar rubutu mai kyau, ta wallafa hoton littafinta

- Wata 'yar Najeriya, Maryam Shehu, ta haddasa cece-kuce mai ban sha'awa game da yin rubutu da fasahar rubutun hannu a makarantu

- Da take wallafa rubutunta mai tsananin kyau, matashiyar ta yi alfahari sannan ta kalubalanci duk wanda ya ga zai iya da ya shiga gasa

- Yayin da 'yan Najeriya da yawa suka yaba mata, wasu sun ce ba lallai ne ta iya wannan rubutu mai kyau ba a yayin karantawa tana rubutawa

Wata matashiya yar Najeriya, Maryam Shehu, ta baiwa mutane da yawa mamaki da kyakkyawan rubutunta yayin da ta nemi wanda yake ganin ya isa su zo suyi gasa.

A wani sako da ta wallafa a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu, budurwar ta sanya ɗaya daga cikin litattafanta na makaranta don nuna baiwar da Allah ya yi mata na iya rubutu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Arewa ga mutanen Arewa: Kada ku kai wa ‘yan kudu hari a arewa

Budurwa ta kalubalanci mutane da su shiga gasar rubutu mai kyau, ta wallafa hoton littafinta
Budurwa ta kalubalanci mutane da su shiga gasar rubutu mai kyau, ta wallafa hoton littafinta Hoto: @fulani_maryaam
Source: Twitter

Wasu mabiya shafin Twitter da suke ganin suma gwanaye ne a wajen rubutu suma sun wallafa nasu.

Lokacin da mutane suka ce lamarin zai sha bamban idan ana karanto mata tana rubutawa, sai budurwar ta nuna musu ba haka ba inda ta sake wallafa hoton wani rubutun nata.

Kalli wallafarta a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin a kasa:

@unilorinamebor ya ce: "Baba wai a inda kuke samun irin wannan kyawawan rubutu a koda yaushe. Ni nawa kamar tsuntsu na caccakar ƙasa."

@lukmanadeola2 ya ce: "Zan so in ga rubutunki a lokacin da malamin makarantar sakandaren da ke jin yunwa ke karanto maki jawabai kina rubutawa."

@Nigerianbreed20 ya ce: "Na tabbata ba rubutun ana fada kina rubutawa bane! saboda rubutunki ba zai kyan wannan ba yayin da malami ke fada kina rubutawa.... Ko yaya dai yayi kyau!"

A wani labarin, Yan Najeriya sun kwararawa wata budurwa sakonnin taya murna ga kyakkyawar budurwa yar Arewa bisa nasaran da ta samu.

KU KARANTA KUMA: Fargaba ya cika Neja bayan masu satar mutane sun saki bidiyon matafiyan da aka sace, sun nemi a biya N500m

Budurwar mai suna Maryam Musa ta yi sanarwa a shafin Tuwita bisa kammala karatun digirinta a fannin karatun lauya.

Maryam, wacce bata bayyana jami'ar da ta kammala ba ta godewa Allah bisa nasarar da ta samu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel