UNN ta dakatar da malami, hukuma ta damke shi a kan dirkawa daliba ciki

UNN ta dakatar da malami, hukuma ta damke shi a kan dirkawa daliba ciki

- UNN ta dakatar da wani malaminta sakamakon zarginsa da dirkawa daliba ciki

- Kamar yadda wasikar dakatarwar ta bayyana, za a cigaba da biyan malamin rabin albashinsa

- An gano cewa bayan dakatar da shi, hukumar ta kama shi kafin a kammala binciken

Wani malami a jami'ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) da ke jihar Enugu, Dr Chigozie Jude Odum an dakatar da shi kuma an damke shi sakamakon cikin da ya dirkawa dalibar jami'ar.

An mayar da cewa za a dinga biyan malamin rabin albashi har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

An bayyana wannan hukuncin ne a wata wasika mai kwanan wata 15 ga Fabrairun 2021 wacce mataimakiyar rijistra ta makarantar, Mrs F. C Achiuwa tasa hannu.

KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce

An dakatar da malamin jami'a a kan zargin dirkawa dalibarsa ciki, an zabtare masa albashi
An dakatar da malamin jami'a a kan zargin dirkawa dalibarsa ciki, an zabtare masa albashi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Wasikar, wacce bata sanar da cewa dirkawa daliba ciki malamin yayi ba, ta ce an dakatar da malamin ne sakamakon zarginsa da ake yi da hantarar daliba tare da cin zarafinta.

Amma kuma, majiya makusanciya da jami'ar ta bayyana cewa malamin ya shiga wannan matsalar ne bayan ya dirkawa dalibarsa ciki.

Majiyar bata bada karin bayani ba a kan yadda lamarin ya auku, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Ana saura makonni 3 auren sojan Najeriya, 'yan bindiga sun sheke shi har lahira

A wani labari na daban, gwamnonin yankin arewa maso yamma a ranar Litinin sun sha alwashin yin amfani da duk wasu hanyoyin da za su iya wurin bai wa rayuka da kadarori kariya a yankin.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya tabbatar da hakan a Kaduna yayin wani taro da ofishin mai bai wa kasa shawara a fannin tsaro ya hada, Vanguard ta wallafa.

Masari wanda yayi jawabi a madadin dukkan takwarorinsa, ya ce tsaro a yankin ya tabarbare don haka dole ne gwamnonin su yi aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel