Gwamnonin arewa maso yamma sun gana da mai bada shawara kan tsaron kasa

Gwamnonin arewa maso yamma sun gana da mai bada shawara kan tsaron kasa

- Gwamnonin yankin arewa maso yammacin Najeriya sun yi taro da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa a kan harkar tsaro

- Kamar yadda gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana, ya ce ya zama dole su kasance masu bai wa yankunansu tsaro

- Masari ya kara da jaddada cewa babu shakka za su yi duk abinda ya dace wurin tabbatar da su tsare yankin daga harin 'yan ta'adda

Gwamnonin yankin arewa maso yamma a ranar Litinin sun sha alwashin yin amfani da duk wasu hanyoyin da za su iya wurin bai wa rayuka da kadarori kariya a yankin.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya tabbatar da hakan a Kaduna yayin wani taro da ofishin mai bai wa kasa shawara a fannin tsaro ya hada, Vanguard ta wallafa.

Masari wanda yayi jawabi a madadin dukkan takwarorinsa, ya ce tsaro a yankin ya tabarbare don haka dole ne gwamnonin su yi aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga na tara kudin siyan makami mai linzami na harbo jiragen sama, Gumi

Gwamnonin arewa maso yamma sun gana da mai bada shawara kan tsaron kasa
Gwamnonin arewa maso yamma sun gana da mai bada shawara kan tsaron kasa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Hakki ne da ke kanmu na mu tabbatar da taron kowa don haka kowanne. Dole ne mu koma yankunanmu, mu gyara su sannan komai ya dawo lafiya," yace.

"A shekaru goma da suka gabata, lamarin bai yi munin haka ba. Amma a yau komai ya tabarbare," Yace.

Masari yayi kira ga dukkan gwamnonin kasar nan da su dauka alhakin kare kowa da ke kasansu ba tare da duban kabila ko addinin ba.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ku yi addu'a Ubangiji ya kawowa Najeriya sauki, Sarkin Bauchi

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari Shagari quarters dake karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina, inda suka kashe shugaban 'yan sa kai dake wurin, Ali Bahago, bayan musayar wuta da suka yi.

'Yan bindigan sun yi garkuwa da wani Mr. Alex, ma'aikacin banki da yaran wani tsoho Hassan, wanda take a wurin ya fadi ya mutu.

Wani mazaunin quarters din wanda babu abinda ya faru dashi a ranar, Sagir Mohammed, ya sanar da ThisDay a ranar Juma'a cewa 'yan bindigan sun shiga quarters din da misalin 11:15pm ranar Alhamis, 11 Fabrairu, kuma sun shafe mintuna 30, inda suka bar ma'aikatan da dama da miyagun raunuka.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel