Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rijistar 'yan APC ta jihar Kwara

Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rijistar 'yan APC ta jihar Kwara

- Lai Mohammed ya bukaci a soke rijistar da ake wa 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Kwara

- Kamar yadda ministan yada labaran ya tabbatar, an take wasu dokokin rijistar yayin yin ta

- Mohammed ya zargi kwamitin rijistar da nuna bangaranci ga wasu masu ruwa da tsakin jam'iyyar

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rijistar 'yan APC da ake yi a jihar Kwara.

A wani taron manema labarai a garinsu na Oro, Mohammed a ranar Litinin ya ce jami'an da aka tura jihar domin sabunta rijistar 'yan jam'iyyar da yi wa marasa rijistar sun yi karantsaye ga dokokin da aka gindaya musu.

Ya ce kwamitin sun taka dokar da aka gindaya wurin rarrabe kayan aikin, Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: 'Yan bindiga: Sanata ya ja kunnen gwamnonin arewa a kan sasanci

Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rijistar 'yan APC ta jihar Kwara
Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rijistar 'yan APC ta jihar Kwara. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Ya bukaci a soke rijistar jam'iyyar da ake yi a jihar Kwara kuma a saka dokokin da suka dace wurin rijistar gaskiya domin ya kasance an yi abinda ya dace.

Ya kara da zargar kwamitin da nuna bangaranci a fannin rikicin da ake yi a jam'iyyar reshen jihar ta hanyar ware manyan masu ruwa da tsaki da suka tabbatar da samuwar nasarar Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

A kwanakin baya an ji yadda rikici ya barke tsakanin bangaren Gwamnan jihar da ministan yada labaran.

KU KARANTA: 'Yan bindiga na tara kudin siyan makami mai linzami na harbo jiragen sama, Gumi

A wani labari na daban, bayan barkewar rashin tsaro a jihar Kebbi, mataimakin gwamnan jihar, Ismaila Yombe, ya koma masarautar Zuru don kawo karshen ayyukan 'yan sa kai a wurin.

Cikin 'yan kwanakin nan, ana zargin 'yan sa kai da tsoratar da alkalai da lauyoyi wadanda suka yi hukunci wanda bai yi musu dadi ba.

Sannan ana zarginsu da kashe-kashe ba tare da kotu ta bayar da umarni ba, Daily Trust ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: