Da duminsa: Sakamakon jita-jitan alakarsa da APC, Shugabannin PDP sun ziyarci Jonathan

Da duminsa: Sakamakon jita-jitan alakarsa da APC, Shugabannin PDP sun ziyarci Jonathan

- Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun shiga ganawa da tsohon shugaba Goodluck Jonathan

- Ana rade-radin cewa Jonathan na shirin fita daga PDP zuwa APC

- Anyi kira ga jam'iyyar APC ta baiwa dan kudu tikitin takara a 2023

Cikin yunkurin dinke barakar dake cikin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP, shugabannin jam'iyyar sun kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Kwamitin sulhu na musamman karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ne suka kai masa wannan ziyara.

A bara, jam'iyyar PDP ta kafa kwamiti na musamman domin sulhu tsakanin 'yayanta.

Daga cikin mambobin kwamitin akwai tsohon sakataren gwamnatin tarayya Anyim Pius Anyim, da tsohon gwamnan Cross River, Liyel Imoke, dss.

Sauran mambobin sun hada da tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo; tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shema, da Hon Mulikat Akande.

Saraki ya sanar da wannan ganawar ta yau a shafinsa na Tuwita, @bukolasaraki.

"A yunkurinmu na sauraron manyan masu ruwa da tsaki a jam;iyyarmu, da ranan nan, kwamitin sulhun PDP na ganawa da tsohon shugaban kasa, H.E. Goodluck Ebele Jonathan (@GEJonathan),” Saraki yace.

KU KARANTA: Jerin wadanda suka rike mukamin shugaban hukumar EFCC a tarihin Najeriya

DUBA NAN: Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu

A bangare guda, Goodluck Jonathan ya ce har yanzu yana nan a PDP inda ya ce "jam'iyyar tana tafiya tare da kowa."

Jonathan ya yi wannan jawabin ne a taron ban godiya da gwamnan jihar Bayelsa Sanata Douye Diri ya yi a Ecumenical Centre da ke Yenagoa a karshen mako.

Kalamansa, "PDP jam'iyya ce da ke haba-haba da kowa. Ni dan jam'iyyar PDP ne kuma na san hakan tun daga farko har zuwa yau. Jam'iyya ce mai tafiya tare da kowa kuma ya kamata mu wanzar da wannan a jihar Bayelsa, hakan ya fara daga jihar Bayelsa saboda duk wadanda ke siyasa daga karshe su hada kai domin mu yi aiki don cigaban mutanen mu.""

Source: Legit.ng

Online view pixel