Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu

Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu

- Bashir Ahmad hadimin Shugaban kasa a kafofin sadarwa na zamani, ya karyata rahoton basa mukami a hukumar DPR

- Sai dai kuma, Bashir ya ce ba zai dauki kowani mataki a kan kafar yada labaran da ta kagi wannan labari na karya ba

- Hakazalika ita ma hukumar da harkokin man fetur ta kasa ta yi watsi da rahoton

Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya yi martani a kan wani rahoton kafar yada labarai da ke cewa an bashi mukami a Hukumar Kula da Harkokin Man fetur ta kasa (DPR).

A hirar da Legit Hausa tayi dashi, Bashir ya ce sam wannan rahoto babu kamshin gaskiya a cikinta don wani abu makamacin haka bai faru ba.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Tsohon Shugaban kasa ya yi martani a kan tashin hankalin da ke kasar

Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun karyata batun
Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun karyata batun Hoto: @bbchausa
Source: Twitter

Da aka nemi ya yi tsokaci, Bashir ya ce:

“Toh har yanzu ma abunda zan ce ba gaskiya bane, ga dai kuma mai tunani, ku yan jarida ne, kun san yanda abubuwa suke, wannan ma inda yan Najeriya za su iya yin tambayar da ya dace, da ba a zo nan ba.

"Babu yanda za a yi a zo da irin wannan takarda a ce wasika ce ta daukar aiki a ma’aikatar gwamnati. Sun dai kagi takardar ne, idan kuka duba za ku ga takardar da DPR suke amfani da ita ba irin wannan bane. Kuma abu guda daya mutum ma zai gane shine wa ya taba ganin Shugaban hukuma ya sanya hannu a takardar daukar aikin ma’aikaci? Ina sashin kula da jin dadin ma’aikata suke? Ina Shugaban ma’aikatansu yake?

"Wannan abubuwan da dama sune za su nuna cewa mu mun dauki abu ne a Nariya idan aka buga labarin karya a kan ka kai ake tunani ka zo ka wanke kanka, ba zama a yi wa wadanda suka sa labarin karyan tambayoyi ba, shine abunda ke yake ban mamaki.

"Da ace za mu ke mayar da hankali idan mutum ya sa labarin karyan, sai mu dunga yi mai tambaya sannan a matsayinku na yan jaridu, ku dauki takardar ku kalle ta, ku duba ku yi bincikenku, ku gano haka DPR suke yi? Menene haka tsarin takardar yake? Haka kanen wasikar DPR yake? Toh da za a rage labaran karya. Amma kawai mutum za a bari da daukar mataki, kuma wasu ko mai ka fada masu baza su yarda ba haka bane."

Game da ko zai dauk mataki a kan kafar labaran da ta yada zancen, hadimin Shugaban kasar ya ce:

“Ni dai babu, bana tunanin akwai wani mataki da zan dauka, zan bar shi ne kowa yayi sharhinsa. Akwai mutanee da dama idan su DRP a matsayinsu na hukuma ko shi Shugaban DPR, Sarki Auwalu yana ganin abunda aka yi masa bai kamata ba zai dauki mataki. Ni na fadi nawa jiya na fito na ce karya ne ba haka bane, idan mutum na da wata shaidar da zai kawo cewa haka ne toh shikenan.”

A nata bangaren, hukumar DPR ta yi watsi da wata takarda da ke yawo a kafofiin sadarwa da ke nuna cewa ta dauki Bashir aiki.

Hukumar ta musanta hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu na wasu yan majalisa biyu

An ta yawo da takardar a shafukan sada zumunta na Intanet da ke dauke da sa hannun shugaban hukumar.

DPR ta ce labarin karya ne kuma aikin wasu bata-gari da ke fakewa da kafofin sada zumunta na intanet domin karkatar da hankalin jama'a.

Sanarwar ta kuma yi kira ga jama'a su yi watsi da takardar daukar aikin wacce ta ce ba ta fito daga DPR ba.

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin zababben shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.

Bawa, dan shekara 40 ne kuma yana daya daga cikin sabbin dauka a hukumar EFCC a 2005.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel