Miji ya yiwa matarshi wanka da tafasashen mai, saboda taki yarda ta koma gidanshi

Miji ya yiwa matarshi wanka da tafasashen mai, saboda taki yarda ta koma gidanshi

- Wata mata mai shekaru 24 ta shiga mummunan hali bayan da tsohon mijinta ya watsa mata tafasasshen ruwa da man girki

- Ta bayyana yadda tsohon mijin nata da suka fi shekara daya da rabuwa, ya sameta a shagon gyaran jikinta da bukatar ta koma gidanshi

- Ya dawo dauke da babban kofin dake kunshe da ruwa tafasasshe da man girki, inda ya watsa mata daga kanta har kasa

Wata mata mai shekaru 24 ta salube bayan da mijinta ya watsa mata tafasasshen ruwa hade da soyayyen man girki.

Matar mai suna Winnie Wambua ta yi ikirarin cewa, tsohon mijin nata mai matsakaicin shekaru mai suna Henry Mugonda, sun rabu dashi ne fiye da shekara daya da ta shude. Ya risketa ne a wajen gyaran jiki a Kiembeni, yankin Kisauni, kuma ya bukaci ta dawo su cigaba da zaman aurensu.

A kalamanta, “A ranar 13 ga watan Disamba, ya zo wajen aikina kuma ya bukaceni da in koma aurenshi. Kamar dai yadda na saba, na ce mishi a’a. Ai kuwa hakan ya harzuka shi kuma ya ce min sai ya tabbatar da na wahala kamar yadda yake jin radadin rasa ni a rayuwarshi.

KU KARANTA: Babu gaira babu dalili aboki ya daddatsa abokinshi da adda, jim kadan da kammala cin abincin su

“Daga nan ne ya fita daga wajen gyaran jikin ya shiga wani wajen saide-saide. Ban san dalilin da na ganshi da risho ba,” Wambua ta ce.

“Bayan kamar mintuna 30, ya koma wajen gyaran jikin dauke da babban kofi da ke kunshe da ruwan zafi da soyayyen man girki. A nan take ya wankeni da wannan abun dake cikin kofin,” cewar Wambua.

Ta kara da cewa, “kamar yadda ya bayyana a aikace, ya shirya hakan tuntuni.”

Tuni dai aka cafke wanda ake zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel