Ina nan daram-dam a jam'iyyar PDP, in ji Goodluck Jonathan

Ina nan daram-dam a jam'iyyar PDP, in ji Goodluck Jonathan

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa har yanzu yana nan a jam'iyyar PDP

- Goodluck ya bada wannan tabbacin ne a yayin da wasu ke hasashen cewa yana shirin komawa APC

- Jonathan ya ce jam'iyyar PDP jam'iyya ce da ke haba-haba da kowa kuma ya shawarci sauran yan jam'iyyar su cigaba da hada kai

A yayin da ake hasashen cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai fice daga jam'iyyar PDP ya koma APC, tsohon shugaban kasar ya ce har yanzu yana nan a PDP inda ya ce "jam'iyyar tana tafiya tare da kowa."

Jonathan ya yi wannan jawabin ne a taron ban godiya da gwamnan jihar Bayelsa Sanata Douye Diri ya yi a Ecumenical Centre da ke Yenagoa a karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Ina nan daram-dam a jam'iyyar PDP, in ji Goodluck Jonathan
Ina nan daram-dam a jam'iyyar PDP, in ji Goodluck Jonathan. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Rabo na da cin abinci tun ranar Juma'a', Ɗan kasuwa ya yi magana kan rikicin Shasa

Kalamansa, "PDP jam'iyya ce da ke haba-haba da kowa. Ni dan jam'iyyar PDP ne kuma na san hakan tun daga farko har zuwa yau. Jam'iyya ce mai tafiya tare da kowa kuma ya kamata mu wanzar da wannan a jihar Bayelsa, hakan ya fara daga jihar Bayelsa saboda duk wadanda ke siyasa daga karshe su hada kai domin mu yi aiki don cigaban mutanen mu."

Tsohon shugaban kasar ya shawarci yan siyasa su sulhunta tsakaninsu bayan zabe su manta da siyasar kiyayya, inda ya kara da cewa bai kamata a rika daukan takara tamkar yaki ba.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah

Jonathan ya cigaba da yin hudubar hadin kai da yi wa al'umma hidima ga yan siyasa inda yace muhimmin abu shine samar da cigaba da al'umma ba rikici ko gaba ba.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel