Allah ya yi wa Sanata Etang Umoyo rasuwa

Allah ya yi wa Sanata Etang Umoyo rasuwa

- Sanata Etang Umoyo daga jihar Akwa Ibom ya riga mu gidan gaskiya

- Tsohon dan majalisar ya rasu ne a ranar Asabar 13 ga watan Fabrairu

- Sanata Umoyo na daga cikin wadanda aka kafa jam'iyyar PDP da su

Etang Umoyo, sanata mai wakiltar mazabar Akwa Ibom ta Kudu a zamanin jamhuriya ta uku da aka rushe ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, LIB ta ruwaito.

Tsohon sanatan wanda ya yi fama da rashin lafiya na wani lokaci ya rasu ne a ranar Asabar13 ga watan Fabarairun shekarar 2021 kamar yadda iyalansa suka sanar a ranar Litinin 15 ga watan Fabarairu.

Allah ya yi wa Sanata Etang Umoyo rasuwa
Allah ya yi wa Sanata Etang Umoyo rasuwa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun sace amarya da ango a lokacin bikin aurensu

Umoyo yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar 2017.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah

Daga bisani ya sake dawowa jam'iyyar PDP a shekarar 2018, inda ya yi ikirarin cewa ya yi hakan ne domin taimakawa Gwamna Udom Emmanuel ya zarce karo na biyu kan karagar mulki.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel