Ana saura makonni 3 auren sojan Najeriya, 'yan bindiga sun sheke shi har lahira

Ana saura makonni 3 auren sojan Najeriya, 'yan bindiga sun sheke shi har lahira

- Rundunar sojin saman Najeriya sun yi arangama da gagararrun 'yan bindiga a wani samame da suka kai a Kaduna

- Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani, ya bayyana yadda aka kashe soja ana sauran makonni 3 aurensa

- A koda yaushe ayyukan ta'addanci na 'yan bindiga kara kamari suke yi a arewa maso gabas na kasar nan

Wani sojan sama na Najeriya ya rasu sakamakon artabu da 'yan bindiga a jihar Kaduna. Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani, ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Ya sanar da yadda 'yan bindigan suka kashe Abubakar Muhammad Ahmad tare da wasu abokan aikinsa a babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Sani ya bayyana cewa sojan na shirye-shiryen aurensa a makonni uku masu zuwa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke Ali Bahago, wani shugaban 'yan sa kai a Katsina

Ana saura makonni 3 auren sojan Najeriya, 'yan bindiga sun sheke shi har lahira
Ana saura makonni 3 auren sojan Najeriya, 'yan bindiga sun sheke shi har lahira. Hoto daga @Shehusani
Asali: Twitter

Ya ce ya yi ta'aziyyar marigayin sojan a gidansu da ke Kaduna a ranar Lahadi, 14 ga watan Fabrairun 2014.

Tsohon dan majalisar ya ce: "Sojan sama Abubakar Muhammad Ahmad tare da wasu abokan aikinsa sun rasu sakamakon harin 'yan bindiga a babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

"Zai yi aure nan da makonni uku. Na ziyarci iyayensa a Kaduna domin ta'aziyya. Allah yayi mishi rahama. Amin."

KU KARANTA: 'Yan bindiga: Sanata ya ja kunnen gwamnonin arewa a kan sasanci

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun halaka gagararrun kwamandoji biyu na Boko Haram, Abul-Bas da Ibn Habib a Banki, kusa da Pulka a jihar Borno kamar yadda PM News ta wallafa.

Kamar yadda aka gano, kwamandojin biyu tare da masu tsaronsu da mayaka duk an kashe su a ranar Juma'a bayan sojin Najeriya sun kai musu hari.

Abul-Bas da Ibn Habib na daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram amma na bangaren Shekau wadanda ke ta'adi a dajin Sambisa da kewaye.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng