Yanzun nan: Ana artabu tsakanin Sojoji da yan Boko Haram a Marte

Yanzun nan: Ana artabu tsakanin Sojoji da yan Boko Haram a Marte

TVC ta ruwaito cewa dakarun Sojojin Najeriya yanzu haka suna artabu da yan ta'addan Boko Haram (ISWAP) a karamar hukumar Marte, jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoton ta bayyana cewa Sojojin sun samu nasarar ceton mutanen da yan ta'addan suka sace amma har yanzu ba'a san adadin rayukan da aka rasa ba.

Marte na yammacin tafkin Chadi, inda rikicin Boko Haram yayi kamari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel