Rashin tsaro: Mataimakin gwamnan Kebbi ya koma Zuru da zama
- Bayan ganin yadda tsaro ya tabarbare a jihar Kebbi, mataimakin gwamna ya dauki tsauraran matakai
- Mataimakin Gwamnan jihar, Ismaila Yombe ya kwashe ya-nashi ya-nashi ya koma masarautar Zuru
- Sannan ya yanke shawarar kawo karshen ta'asar da 'yan sa kai suke yi a fadin jihar
Bayan barkewar rashin tsaro a jihar Kebbi, mataimakin gwamnan jihar, Ismaila Yombe, ya koma masarautar Zuru don kawo karshen ayyukan 'yan sa kai a wurin.
Cikin 'yan kwanakin nan, ana zargin 'yan sa kai da tsoratar da alkalai da lauyoyi wadanda suka yi hukunci wanda bai yi musu dadi ba.
Sannan ana zarginsu da kashe-kashe ba tare da kotu ta bayar da umarni ba, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Bidiyon budurwa mai tsohon ciki da saurayi a Turai suna fada a titi, ya ce ba cikinsa bane
Yombe ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin tattaunawa da manema labarai a Birnin Kebbi inda ya bayar da umarni ga yan sa kai da su yi gaggawar bayyana bara-gurbin dake cikinsu wadanda suke ganganci da hukuma.
Mataimakin gwamnan ya bayyana bacin ransa da rashin bin dokar 'yan sa kai a wurin, inda yace idan har suka ki bayyana masu laifin cikinsu tabbas gwamnati za ta gyara musu zamansu.
Yombe ya bai wa kwamishinan shari'a tabbaci bisa harin da aka kai wa wani lauya a wurin kuma ya lashi takobin kawo karshen ayyukan yan sa kai wanda da farko an kirkiri kungiyar ne don taimako wurin kawo zaman lafiya a anguwanni.
"Babu wata gwamnati da za ta tsaya tana kallo ana cutar da al'ummarta. Na samu ganawa da yan sa kai kuma na tuna musu asalin dalilin da ya sanya aka kirkiri kungiyar.
"Na umarce su da suyi gaggawar fitar da baragurbin da suke cikin su kafin gwamnati ta dauki mummunan mataki," a cewarsa.
KU KARANTA: Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje
A wani labari na daban, Farfesa Umar Labdo sakataren kungiyar samar da cigaban Fulani ne wato FULDAN, sannan kuma farfesa ne a bangaren siyasar musulunci a jami'ar Yusuf Maitama Sule dake jihar Kano.
A wata tattaunawa da aka yi da shi ya bayyana tushen rikicin makiyaya da manoman kasar nan da kuma yadda za a shawo kan lamarin.
Kamar yadda yace, "Yadda aka bai wa Fulani kwanaki su tattara kayansu ba a kyauta ba, in dai har ana neman zaman lafiya. Akwai Yarabawa da suke damfara a yanar gizo da Ibo da suke sayar da miyagun kwayoyi a jihata wacce nake zama a arewa. Kuma suna zaune lafiya sana sana'o'insu babu wanda yace su kwashe kayansu."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng