'Yan bindiga: Sanata ya ja kunnen gwamnonin arewa a kan sasanci

'Yan bindiga: Sanata ya ja kunnen gwamnonin arewa a kan sasanci

- Sanata mai wakiltar Cross River ta kudu ya bai wa gwamnonin arewa shawara a kan sasanci da 'yan bindiga

- Ya ce duk da sasanci yayi amfani a kan tsagerun kudancin Najeriya, amma kada su sasanta da 'yan bindiga

- Sanatan ya bukaci kasar nan da ta dinga amfani da fasahar zamani wurin shawo kan matsalar garkuwa da mutane

Sanata Gershom Bassey, sanata mai wakiltar jihar Cross River ta kudu a jiya yayi kira ga gwamnonin arewa da su kasance masu taka-tsan-tsan wurin sasanci da 'yan bindiga.

A yayin jawabi ga manema labarai a Abuja, ya ce duk da shirin rangwame na fadar shugaban kasa ya yi kokari wurin rage aikin tsagerun kudancin Najeriya, akwai abun damuwa a bangaren sasanci da 'yan bindiga.

Ya ce idan aka yi amfani da salon fasahar zamani, laifuka da masu yin su duk za su ragu, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheke Abul-Bas da Ibn Habib, manyan kwamandojin Boko Haram

'Yan bindiga: Sanata ya ja kunnen gwamnonin arewa a kan sasanci
'Yan bindiga: Sanata ya ja kunnen gwamnonin arewa a kan sasanci. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

"Baka gani ko jin labarin masu garkuwa da mutane a wasu kasashe, saboda mene? Saboda fasahar zamani. Idan akwai fasahar zamani, garkuwa da mutane tana zama abu mai matukar wahala," yace.

KU KARANTA: Bidiyon budurwa mai tsohon ciki da saurayi a Turai suna fada a titi, ya ce ba cikinsa bane

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci nauyin da ke kan shugabannin gargajiya ba, musamman shugaba irin na babbar masarauta irin ta Kano.

Ganduje ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Channels suka yi da shi. Inda suka bukaci sanin dalilan da suka sanya ya tube wa sarkin rawaninsa lokacin yana kan karagar sarautar Kano.

A cewar Ganduje, "Tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci rawar da shugabannin gargajiya ya kamata su dinga takawa ba."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel