Masu garkuwa sun sace amarya da ango a lokacin bikin aurensu

Masu garkuwa sun sace amarya da ango a lokacin bikin aurensu

- Masu garkuwa da mutane sun sace wasu masoya da aka shirya yin aurensu ranar Asabar a Delta

- Bayan sace su, masu garkuwar sun nemi a biya Naira miliyan 15 na kudin fansa kafin su sako su

- An yi kokarin tuntubar kakakin yan sandan jihar Delta domin jin karin bayani amma hakan ya ci tura

Yan bindiga da ake zargin makiyaya Fulani ne sun sace amarya da ango da aka shirya daura aurensu a ranar 13 ga watan Fabarairu a Emuhu, Agbor, karamar hukumar Ika South na jihar Delta, The Punch ta ruwaito.

An gano cewa wadanda suka sace su sun nemi a biya su Naira miliyan 15 kudin fansa kafin su sako amarya da ango da ba a bayyana sunansu ba kawo yanzu.

DUBA WANNAN: Labari da ɗumi-ɗumi: Sanata Iyiola Omisore ya koma jam'iyyar APC

Wata majiya a garin ya ce, "Makiyaya Fulani sun sace masoyan da aka shirya yin aurensu ranar Asabar da ta gabata, tare da wani a Railway Emuhu Agbor; suna neman a biya su Naira miliyan 15 kafin su sako su.

"Akwai dimbin yan sanda da sojoji da wasu jami'an tsaro a garin Ika amma ba su iya tabuka komai ba game da yawaitar satar mutane da ake yi. Ka duba wadanda ya kamata su yi aure su more rayuwarsu an sace su. Abin ba dadi.

"Yanzu suna neman a biya kudi kafin su sako su. Ta ina za su samo irin wannan kudin?."

KU KARANTA: Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

An yi kokarin ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya amma ba bai amsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel