'Rabo na da cin abinci tun ranar Juma'a', Ɗan kasuwa ya yi magana kan rikicin Shasa
- Wani bahaushe cikin yan kasuwa da ke garin Sasha a jihar Oyo ya magantu kan halin da ya shiga bayan rikicin da ta barke
- Dan kasuwar ya ce ya shafe kimanin kwanaki uku rabonsa da cin abinci kwakwara sakamakon rikicin na kasuwar Sasha
- Dan kasuwar ya ce ya rasa dukiyarsa da kadarorinsa inda ya yi kira ga gwamnati ta yi gaggawan kai musu dauki
Daya daga cikin yan kasuwar da rikicin Sasha a karamar hukumar Akinyele ta jihar Oyo, ya ce rabonsa da cin abinci kwakwara tun ranar Juma'a da ta gabata.
A hirar da aka yi da shi da Daily Trust, dan kasuwan da ya nemi a sakayya sunansa ya ce ya rasa dukkan abinda ke cikin shagonsa sakamakon rikicin.
KU KARANTA: Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan
Ya bada labarin yadda bata gari suka kai masa hari, inda ya nemi gwamnati ta kawo musu dauki.
"Rabo na da cin abinci tun ranar Juma'a. Abubuwan sha kawai na ke lalabawa. Gwamnati ta gaggauta kawo mana taimako. Na rasa komai a shago na ban ma san iya adadin asarar da na yi ba," in ji shi.
A bangarensa, Abdu Tanko, wani dan kasuwa da rikicin ta shafa, ya bayyana yadda ya yi asarar albasa da kudinta ya kai Naira miliyan 3.
Tanko ya ce bata gari sun lalata albasar da ya yi oda daga Sokoto zuwa Legas.
DUBA WANNAN: Labari da ɗumi-ɗumi: Sanata Iyiola Omisore ya koma jam'iyyar APC
Daya daga cikin matan da suka rabe a gidan sarkin Sasha, shugaban hausawar garin ta bayyana wahalar da ta fuskanta.
Ta ce an kore su daga gidajensu, an musu duka, an kashe wasu daga cikinsu an kuma kone gidajensu da kadarorinsu.
A kalla mutane 20 ne aka kashe yayin da aka bannatar da kadarori na miliyoyin naira sakamakon rikicin da ta barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Sasha.
A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.
Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.
Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng