Kashe-kashe: Gwamnonin Jihohin Arewa sun hadu a Kaduna, sun shiga muhimmin taro

Kashe-kashe: Gwamnonin Jihohin Arewa sun hadu a Kaduna, sun shiga muhimmin taro

- Gwamnoni su na yin wani zama na musamman kan harkar tsaro a jihar Kaduna

- Gwamnonin na Arewa su na duba rikicin da ya barke a wani bangaren Jihar Oyo

- Nasir El-Rufai ya ce ana yin wannan zama ne a gidan Arewa House da ke Kaduna

Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna, inda su ke tattauna wa game da abubuwan da su ke faru wa game da rikicin Oyo.

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bada sanarwar wannan taro a shafinsa na Twitter.

Rahotannin da mu ke samu shi ne, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne da kimanin karfe 12:00 na ranar yau, Litinin, 15 ga watan Fubrairu, 2021.

Ana wannan zama ne a gidan taro na Arewa House da ke garin Kaduna, a karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong.

KU KARANTA: Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan mutane a Shasha

Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong shi ne jagoran gwamnoni 19 na yankin Arewacin Najeriya.

Kamar yadda gwamnan na Kaduna ya bayyana, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro ne ya bukaci ayi wannan muhimman zama a Kaduna.

Hotuna sun tabbatar da cewa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Abubakar su na wajen wannan muhimmin taro.

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya na cikin wadanda su ka halarci wannan zama, sai dai ba mu da cikakken adadin wadanda su ka halarci zaman.

KU KARANTA: Kisan da ake yi wa mutanen Arewa a Jihar Oyo bai dace ba - Gwamna

Kashe-kashe: Gwamnonin Jihohin Arewa sun hadu a Kaduna, sun shiga muhimmin taro
Gwamnonin Jihohin Arewa Hoto:@GovKaduna
Source: Twitter

Har ila yau, taron ya samu halartar mata da masu sarautar gargajiya, wannan duk a kokarin da ofishin NSA yake yin a ganin an kade tashin fitina a Najeriya.

A jiya, an ji mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro, Babagana Monguno, ya na cewa gwamnatin tarayya ta damu da matsalolin tsaro da ake fama da su.

Tawagar NSA za ta fara rangadi zuwa sassan Najeriya daga ranar Litinin domin a samu zaman lafiya.

Monguno ya ke cewa an kirkiro wannan tsari ne na ganawa da gwamnoni, sauran shugabannin da masu ruwa da tsaki ne domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel