Gwamnan Zamfara ya fito ya soki kisan da ake yi wa mutanen Arewa a Jihar Oyo

Gwamnan Zamfara ya fito ya soki kisan da ake yi wa mutanen Arewa a Jihar Oyo

- Gwamnan Jihar Zamfara ya yi tir da irin harin da ake kai wa ‘Yan Arewa a Oyo

- Bello Matawalle ya bukaci gwamnatin tarayya da ta Oyo su magance matsalar

- Gwamnan ya yi magana ne ta bakin wani hadiminsa, Mallam Zailani Bappa, jiya

Mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi matukar Allah-wadai da harin da ake kai wa mutanen Arewa a Ibadan, jihar Oyo.

Daily Trust ta ce gwamna Bello Mohammed Matawalle ya fitar da jawabi ta bakin mai taimaka masa wajen hulda da jama’a da sada labarai, Zailani Bappa.

Gwamnan ya jajanta wa wadanda wannan rikici ya kaure da su, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da zai kashe wutan rikicin.

“Babu wani uzuri da za a bada na cewa a irin wannan yanayi, a matsayinmu na kasa, har yanzu ba mu gane cewa Ubangiji ya yi nufin mu zauna a dunkule ba.”

KU KARANTA: Rikicin Oyo: Mutane fiye da 3000 suna boye a gidan Sarkin Shasha

“Abin takaici ne ace a lokacin da sauran abokan tarayyarmu su ke zamansu a lafiya a sauran wurare, mu kuma mu na yin baya.” Inji Gwamna Matawalle.

Bello Matawalle ya yi magana, ya na mamakin inda wannan kiyayya da ake nuna wa zai kai Najeriya, ya ce babu inda wannan dabi’a za ta kai mu sai fitina.

Gwamnan ya yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauki matakai domin kawo karshen karon-tsanan da aka daura wa Fulani a kasar nan.

“Ina kuma kira ga abokin aiki na, gwamnan jihar Oyo, ya dauki matakan da su ka dace domin ganin bayan wannan miyagun hare-hare marasa kan gado.”

Gwamnan Zamfara ya fito ya soki kisan da ake yi wa mutanen Arewa a Jihar Oyo
Gwamnan Zamfara , Bello Matawalle Hoto; @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba zan bari Kungiyoyin addini da kabilu su jawo tashin hankali ba - Buhari

Matawalle ya kara da cewa dole gwamnati ta tabbatar hakan bai sake faru wa ba. A cewarsa masu daukar makamai ne abokan fada ba masu neman na abinci ba.

Kungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta sha alwashin cewa ba za ta bar yankin kudu maso yammacin kasar nan ba duk da rikicin da ake fama da shi.

Sakataren kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa, Alhassan Saleh ya ce kundin tsarin mulki ya basu damar zaben zama a duk yankin da su ka ga dama a Najeriya.

Alhassan Saleh ya yi wannan furuci ne a hirar da yi da Sunday Punch a kan wa'adin da ake ba su.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel