Rikicin kabilanci: NSA Monguno ya bayyana matakin da fadar shugaban kasa ta dauka

Rikicin kabilanci: NSA Monguno ya bayyana matakin da fadar shugaban kasa ta dauka

- Mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro (NSA), Babagana Monguno, ya ce gwamnatin tarayya ta damu da matsalolin tsaro a fadin kasa

- Monguno ya bayyana cewa zai jagoranci wata tawaga da gwamnatin tarayya ta kafa domin tuntubar masu ruwa da tsaki a fadin kasa

- A cewar Monguno, tawagarsa za ta fara rangadi zuwa sassan Nigeria daga ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu

Wata tawaga a karkashin mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Babagana Monguno, za ta fara gudanar da wani rangadi domin neman mafita akan matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasa.

A cikin wata sanarwa da Monguno ya fitar ranar Lahadi, ya ce tawagarsa za ta fara ganawa da gwamnonin jihohin arewa ta yamma a garin Kaduna ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu.

A cewarsa, an kirkiro wannan tsari ne na ganawa da shugabannin da masu ruwa da tsaki domin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasa.

Ana cigaba da samun rahotannin samun yawaitar tashin hankali da kai hare-hare akan 'yan arewa mazauna kudu musamman a yankin kudu maso yamma.

"A kokarin gwamnatin tarayya na ganin ta kawo karshen matsalolin tsaro a sassan kasa, NSA Monguno ya jagoranci wani taro da babban kwamitin harkokin tsaro na kasa (GSAC) a ranar 11 ga watan Fabarairu.

KARANTA: Ba a sulhu da ƴan ta'adda: Jayayya ta barke tsakanin El-Rufai da Sheikh Gumi martani

Rikicin kabilanci: NSA Monguno ya bayyana matakin da fadar shugaban kasa ta dauka
Rikicin kabilanci: NSA Monguno ya bayyana matakin da fadar shugaban kasa ta dauka
Asali: Depositphotos

"Taron ya samu halartar dukkan shugabannin rundunoni da hukumomin tsaro kuma an tattauna akan dukkan kalubalen tsaro da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, 'yan bindiga, da kuma dukkan sauran matsalolin tsaro.

"Domin sabunta kokarin warware wadannan matsaloli, mun yanke shawarar fadada aikinmu ta hanyar fara rangadi domin tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan," a cewar sanarwar da Monguno ya fitar.

A cewar Monguno, tawagarsa zata tattauna da gwamnoni, shugabannin addini, sarakunan gargajiya, 'yan majalisu, kungiyo mazu zaman kansu na maxa da mata da matasa da sauransu.

Monguno ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta matukar damu da abubuwan da suke faruwa kuma tana kokarin inganta tsaro ta hanyar yin aiki da dukkan masu ruwa da tsaki.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Babbar kungiyar Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta ce ta gaji da cin kashi da barazanar da ake yi wa mambobinta kuma a halin yanzu tura ta kai bango.

Rahotanni na cigaba da bayyana yadda ake kara samun yawaitar kai hare-hare akan makiyaya da ke zaune ko xiyartar kudancin Nigeria.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Saleh Alhassan, ya ce makiyayan da ake kashewa daban da wadanda suke tafka barna a sassan Nigeria.

Naziru Dalha Taura Malamin makaranta ne kuma dalibi da ke sha'awar rubuce-rubuce akan dukkan al'amuran da suka shafi jiya da yau. Ya samu kusan shekaru hudu yana aiki da Legit.ng.

Ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano a bangaren ilimin kimiyyar sinadaran rayuwa da tasirinsu a jikin dan adam.

Za'a iya tuntubarsa kai tsaye a shafinsa na tuwita a @deluwa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel