Rashin tsaro: mun gaza sauke nauyin da aka daura mana, in ji Kakaki

Rashin tsaro: mun gaza sauke nauyin da aka daura mana, in ji Kakaki

- Wani kakakin majalisar wakilai ya koka kan yadda al'amuran tsaro suka lalace a Najeriya

- Ya bayyana cewa, 'yan siyasar Najeriya sun gaza wajen sauke nauyin da ke kansu

- Ya kuma kirayesu da su hada kai su kuma kau da kabilanci wajen magance rashin tsaro

Matsalar tsaro a Najeriya ta dauki wani sabon salo a ranar Laraba tare da kashe-kashe da satar mutane a fadin jihohin kasar, The Nation ta ruwaito.

A Abuja, ‘yan majalisar tarayya sun fara gabatar da zaman su na 2020 tare da muhawara kan rashin tsaro a Majalisar Dattawa da wani jawabi mai karfi da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi, wanda ya shafi rashin tsaro.

Gbajabiamila ya koka kan yadda masu rike da mukaman siyasa ke gagara kare rayuka da dukiyoyi duk lokacin da aka sace mutum ko aka kashe shi.

KU KARANTA: IPPIS zamba ne, gwamnati ta yaudare mu ne kawai, inji wani shugaban NASU

Rashin tsaro: mun gaza a sauke nauyin da aka daura mana, in ji Kakakin
Rashin tsaro: mun gaza a sauke nauyin da aka daura mana, in ji Kakakin Hoto: Premium Times
Source: UGC

Ya ce: “Duk lokacin da aka kashe wani dan kasa da ke sauke harkokinsa, ko aka sace shi, aka rusa dukiyoyinsa ko abin da zai ci, yana nuna mun gaza wajen sauke nauyin da ke kanmu.

"Daga yawantar wadannan gazawar ya fito da wata al'ada ta taimakon kai da kai a cikin al'amuran da suka shafi tsaron cikin gida wanda ke haifar da babban hatsari ga ci gaban kasarmu."

Shugaban Majalisar ya kara da cewa: “Idan har akwai lokacin da za mu yi watsi da duk wasu lamura, musamman kananan matsalolin da ke damun bangaranci da siyasa, yanzu ne.

Kakakin ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da ya dace a kawar da bambancin addini, kabila da bangaranci domin ci gaban kasa.

Ya kamata a hada karfi da karfe don shawo kan kalubale na tayar da kayar baya da ta'addanci, tashin hankali a tsakanin al'umma, da kuma tashin hankali a kan kasa; wannan lokacin yanzu ne.” in ji shi.

KU KARANTA: Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma

A wani labarin, Sakamakon umarnin fatattakar makiyaya masu aikata laifuka a wasu jihohin kudu, kimanin makiyaya 4,000 sun bar jihohin kudu zuwa Kaduna, Nigerian Tribune ta ruwaito.

An tattaro cewa makiyayan tun makon da ya gabata suna dawowa zuwa garin Labduga, karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel