Sojin Najeriya sun sheke Abul-Bas da Ibn Habib, manyan kwamandojin Boko Haram

Sojin Najeriya sun sheke Abul-Bas da Ibn Habib, manyan kwamandojin Boko Haram

- Rundunar sojin Najeriya ta halaka manyan kwamandoji biyu da suka gagara na Boko Haram

- Abul-Bas da Ibn Habib sun kasance a jerin miyagun 'yan ta'adda da ke barna a yankin Sambisa da kewaye

- Kamar yadda aka gano, suna daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram na bangaren Shekau

Dakarun sojin Najeriya sun halaka gagararrun kwamandoji biyu na Boko Haram, Abul-Bas da Ibn Habib a Banki, kusa da Pulka a jihar Borno kamar yadda PM News ta wallafa.

Kamar yadda aka gano, kwamandojin biyu tare da masu tsaronsu da mayaka duk an kashe su a ranar Juma'a bayan sojin Najeriya sun kai musu hari.

Abul-Bas da Ibn Habib na daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram amma na bangaren Shekau wadanda ke ta'adi a dajin Sambisa da kewaye.

KU KARANTA: Bidiyon budurwa mai tsohon ciki da saurayi a Turai suna fada a titi, ya ce ba cikinsa bane

Sojin Najeriya sun sheke Abul-Bas da Ibn Habib, manyan kwamandojin Boko Haram
Sojin Najeriya sun sheke Abul-Bas da Ibn Habib, manyan kwamandojin Boko Haram. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Sun kasance a cikin jerin sunayen miyagun da aka dade ana nema na dogon lokaci wadanda daga bisani dakarun rundunar Operation Tura Ta kai Bango suka halaka.

Kamar yadda maijya daga cikin rundnar sojin ta tabbatar, an samu GPMG, bindigogi kirar AK47, harsasai, babura da kuma wayoyi bayan halaka Abul-Bas da Ibn Habib tare da wasu mayaka.

"A gaskiya mutuwar Abul-Bas da Ibn Habib sun yi mummunan lahani a kan ayyukan 'yan ta'adda yayin da hakan ya zama babbar nasara kuma lamarin da zai karfafa guiwar sojojin," sojan ya tabbatar.

"Rundunar sun hada da wasu da dakarun bataliya ta 121 da wasu daga bataliya ta 151 wadanda ake kira da "Gaddafi Squad"," ya kara da cewa.

Kwamandan 7 Division, Manjo Janar Abdul Khalifa yayin jawabi ga kwamandajoji a madadin shugaban sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya yi kira ga dakarun da su tsananta wurin kawar da 'yan ta'adda a Sambisa da kewaye.

KU KARANTA: Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi

A wani labari na daban, Abdullahi Abbas, shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC na jihar Kano, ya umarci duk masu kishin jam'iyyar da su kai wa duk wanda yayi yunkurin yin murdiyar zabe a jihar farmaki.

Abbas ya dade yana bai wa 'yan jam'iyyar kwarin guiwa akan siyasa. Ya ja kunnen 'yan jam'iyyar a wani taro da suka yi a watan Janairu, inda yace akwai mummunan mataki da jam'iyya za ta dauka akan duk wanda bai sake rijistar ba.

Shekarar da ta gabata, jam'iyyar ta shirya yin wani shiri na "violence for violence" akan zaben 2023, The Cable ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: