Bidiyon budurwa mai tsohon ciki da saurayi a Turai suna fada a titi, ya ce ba cikinsa bane

Bidiyon budurwa mai tsohon ciki da saurayi a Turai suna fada a titi, ya ce ba cikinsa bane

- Wani bidiyon wata mata mai tsohon ciki a tsakar titin Turai ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta

- An ga matar a bidiyon tana jan mutumin har take cewa tabbas shine ya dirka mata cikin da yake jikinta

- Sai dai mutumin ya murje ido ya ki amincewa , ita kuma ta ce ba za ta sake shi ba sai ya yarda cewa cikinsa ne a jikinta

Wani bidiyo ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta wanda aka ga wata mata da tsohon ciki a titin Turai tana jan wani mutum da cewa shine yayi mata cikin da yake jikinta.

Duk da yadda ta dage tana cusa masa cikin, amma mutumin ya murje idanunsa yace sam ba nashi bane.

Matar ta dage a tsakar titi tana cacar baki a gaban jama'a tana cewa tabbas shine yayi mata cikin.

KU KARANTA: Sojin Najeriya basu son ganin karshen ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi

Bidiyon budurwa da saurayi a Turai suna rikici a titi a kan cikin da tace ya dirka mata
Bidiyon budurwa da saurayi a Turai suna rikici a titi a kan cikin da tace ya dirka mata. Hoto daga Premiumtimes.com
Asali: UGC

Duk da ya ki amincewa, ta ce baza ta taba sakin shi ba har sai ya tabbatar wa da kowa cewa cikinsa ne, The Nation ta ruwaito.

Wata mata ta shiga al'amarin dumu-dumu kamar yadda aka gani a bidiyon, tana cewa ya kamata mutumin ya yarda da cewa shi ya dirka mata cikin.

Ya tsoratar da matar cewa zai kira mata 'yan sanda don ya ga wandunan wasu maza a gidansa, hakan ce tasa yake tunanin ba cikinsa bane.

KU KARANTA: Kada ku ga laifin makiyaya idan suna yawo da miyagun makamai, Gwamnan Bauchi

A wani labari na daban, Abdullahi Abbas, shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC na jihar Kano, ya umarci duk masu kishin jam'iyyar da su kai wa duk wanda yayi yunkurin yin murdiyar zabe a jihar farmaki.

Abbas ya dade yana bai wa 'yan jam'iyyar kwarin guiwa akan siyasa. Ya ja kunnen 'yan jam'iyyar a wani taro da suka yi a watan Janairu, inda yace akwai mummunan mataki da jam'iyya za ta dauka akan duk wanda bai sake rijistar ba.

Shekarar da ta gabata, jam'iyyar ta shirya yin wani shiri na "violence for violence" akan zaben 2023, The Cable ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng