'Yan bindiga sun sheke Ali Bahago, wani shugaban 'yan sa kai a Katsina

'Yan bindiga sun sheke Ali Bahago, wani shugaban 'yan sa kai a Katsina

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari Shagari quarters dake karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina

- Sakamakon harin, sun kashe wani shugaban 'yan sa kan wurin, Ali Bahago, bayan sun yi musayar wuta

- Bayan nan sun yi garkuwa da wani Mr Alex, ma'aikacin banki da wasu 'yan mata guda 2 wanda mahaifinsu ya mutu take a wurin

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari Shagari quarters dake karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina, inda suka kashe shugaban 'yan sa kai dake wurin, Ali Bahago, bayan musayar wuta da suka yi.

'Yan bindigan sun yi garkuwa da wani Mr. Alex, ma'aikacin banki da yaran wani tsoho Hassan, wanda take a wurin ya fadi ya mutu.

Wani mazaunin quarters din wanda babu abinda ya faru dashi a ranar, Sagir Mohammed, ya sanar da ThisDay a ranar Juma'a cewa 'yan bindigan sun shiga quarters din da misalin 11:15pm ranar Alhamis, 11 Fabrairu, kuma sun shafe mintuna 30, inda suka bar ma'aikatan da dama da miyagun raunuka.

KU KARANTA: Bidiyon budurwa mai tsohon ciki da saurayi a Turai suna fada a titi, ya ce ba cikinsa bane

'Yan bindiga sun sheke Ali Bahago, wani shugaban 'yan sa kai a Katsina
'Yan bindiga sun sheke Ali Bahago, wani shugaban 'yan sa kai a Katsina. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

"Yan bindiga sun kai hari Shagari quarters a ranar Alhamis inda suka kashe Alhaji Ali Bahago, shugaban 'yan sa kan wurin. Ya je ne don ya cece mu daga wurin 'yan bindiga amma sun kashe shi sakamakon musayar wutar da suka yi," a cewarsa.

KU KARANTA: Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi

A wani labari na daban, Farfesa Umar Labdo sakataren kungiyar samar da cigaban Fulani ne wato FULDAN, sannan kuma farfesa ne a bangaren siyasar musulunci a jami'ar Yusuf Maitama Sule dake jihar Kano.

A wata tattaunawa da aka yi da shi ya bayyana tushen rikicin makiyaya da manoman kasar nan da kuma yadda za a shawo kan lamarin.

Kamar yadda yace, "Yadda aka bai wa Fulani kwanaki su tattara kayansu ba a kyauta ba, in dai har ana neman zaman lafiya. Akwai Yarabawa da suke damfara a yanar gizo da Ibo da suke sayar da miyagun kwayoyi a jihata wacce nake zama a arewa. Kuma suna zaune lafiya sana sana'o'insu babu wanda yace su kwashe kayansu."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel