Zargin cin amana: PDP ta dakatar da wani shugabanta a jihar Katsina

Zargin cin amana: PDP ta dakatar da wani shugabanta a jihar Katsina

- Jam'iyyar PDP reshen karamar hukumar hukumar Matazu ta jihar Katsina ta dakatar da shugabanta

- Kamar yadda shugabanni da dattawan jam'iyyar suka bayyana, ana zargin Honarabul Karadua da ayyukan cin amana a jam'iyyar

- An maye gurbinsa da Honarabul Jabiru Adamu Rinjin Idi wanda zai yi shugabancin rikon kwarya kafin a kammala bincike

Jam'iyyar PDP ta jihar Katsina reshen karamar hukumar Matazu ta dakatar da shugabanta, Honarabul Murtala Tukur Karadua a kan zarginsa da ayyukan cin amana a jam'iyyar.

An kai ga matsayar dakatar da Honarabul Tukur Murtala Karadua ne a taron da shugabanni da kuma dattawan mazabu 10 na karamar hukumar Matazu suka yi a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairun 2021.

Kamar yadda takardar da Bashir Ibrahim Matazu, jami'in yada labaran jam'iyyar na kafafen sada zumunta ya aikawa da Legit.ng ta bayyana, an yi wannan dakatarwan ne bisa dogaro da sashi na 58 na kudin tsarin mulkin jam'iyyar wanda aka gyara a 2017.

KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

Zargin cin amana: PDP ta dakatar da wani shugabanta a jihar Katsina
Zargin cin amana: PDP ta dakatar da wani shugabanta a jihar Katsina. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: UGC

"Jam'iyyar PDP ta karamar hukumar Matazu ta dakatar da Honarabul Murtala Tukur Karadua a matsayin shugabanta.

"Zai dakata daga shugabancin jam'iyyar har sai an kammala bincike a kan abubuwan da ake tuhumarsa da su kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadar," takardar tace.

Har ila yau, a wannan taron ne shugabanni da dattawan jam'iyyar suka mika ragamar shugabancin jam'iyyar a karamar hukumar hannun Honarabul Jabiru Adamu Rinjin Idi na rikon kwarya.

KU KARANTA: Fani-Kayode ya tunkare ni da batun sauya sheka zuwa APC, Yahaya Bello

A wani labari na daban, Wata kotun majistare da ke zama a Sokoto ta kama wasu matasa da laifin yada bidiyon tsiraicin wata yarinya a kafafen sada zumuntar zamani.

Wadanda ake zargin sune wani Aminu Tafida, da mai ada shawara na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Umar Abubakar da Mas'ud Gidado.

Amma kuma wanda ake zargi na hudu mai suna Aliyu Shehu kangiwa an wanke shi saboda bashi da wata alaka da wannan laifin, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel