'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba

'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba

- Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta musanta kaiwa Soyinka hari da ake cewa makiyaya sun yi

- Kamar yaadda suka bayyana, shanun da suka kutsa cikin gidansa na wani bayerabe ne ba Fulani ba

- Wani bayerabe mai suna Kazeem Sorinola ne ya baiwa bafulatani kiwo kuma wucewa suka je yi

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta sanar da cewa shanun da suka kutsa cikin gidan Wole Soyinka na wani bayerabe ne.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya ce shanun na wani Kazeem Sorinola ne wanda ya dauka wani bafulatani wanda yake kula da shanun.

"Shanun na wani bayerabe ne mai suna Kazeem Sorinola. Ya bai wa wani bafulatani kula da shanun ne. Shanun ba na bafulatanin bane, dan tsaro ne kawai," Oyeyemi yace.

KU KARANTA: Mai gidan haya ya lakadawa 'yar haya mugun duka, ta maka shi a gaban kotu

'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba
'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

The Cable tun farko ta ruwaito cewa Olaokun, dan Wole Soyinka ya musanta rahoton cewa wasu Fulani sun kutsa gidan mahaifinsa da ke yankin Kemta a Abeukuta, jihar Ogun.

Wata muryar bidiyo da ta dinga yawo a kafafen sada zumunta ta yi ikirarin cewa wasu makiyayya sun kutsa gidan Soyinka inda suka dinga mishi barazanar halaka shi.

Amma kuma, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun musanta harin inda suka ce shanu ne kawai suka shiga ta gidan.

KU KARANTA: Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur

A wani labari na daban, Abduljabar Nasir Kabara, babban malamin da gwamnatin Kano ta haramtawa wa'azi ya maka gwamnatin jihar Kotu a kan tsaresa da tayi ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin Kano ta hana Kabara wa'azi a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 a kan zarginsa da wa'azi da zai iya tada zaune tsaye, The Cable ta wallafa.

A ranar 7 ga watan Fabrairu, gwamnatin jihar ta amince da mukabala tsakanin Sheikh Kabara da sauran malaman addini a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng