Zakakuran dakarun soji sama sun yi raga-raga da 'yan bindiga a Birnin Gwari
- Zakakuran sojin saman najeriya sun kai samamen ramuwa a kan 'yan bindiga a jihar Kaduna
- Sojin saman sun yi nasarar ragargaza 'yan bindiga masu tarin yawa a Birnin Gwari da kewaye
- Samamen da sojin suka kai ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa sama da mutum 40 a kwana biyu
Dakarun sojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa a samamen da suka kai ta jiragen yaki a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Wannan samamen ya biyo bayan kisan gilla da 'yan bindiga suka yi wa sama da mutum 40 a kananan hukumomi 5 na jihar a cikin kwana biyu kacal.
Kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, yace an ga 'yan bindigan a Sabon Madada tare da shanu kuma an ragargaza su, Channels TV ta wallafa.
KU KARANTA: Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur
Dakarun sojin sun kashe wasu 'yan bindiga da aka ga suna tsallake dogo da ya hada dajin Kuyambana da Sabon Madada.
Kwamishinan ya bayyana cewa sojin sama sun zagaya da jiragensu ta yankunan Birnin Gwari da suka hada da Goron Dutsee, Sabon Madada, Dan Sadau, Baba Doka, Namaigiya, Danmani, Sani Maichoko da kewaye.
KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ya dace a sani game da sabon kakakin soji, Birgediya Janar Yerima
A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce nada sabbin hafsoshin tsaro da gwamnatin tarayya tayi yasa an samar da sabbin dabaru, hazaka da hanyoyin yakar ta'addanci, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Najerya.
Osinbajo ya sanar da hakan ne a Ikenne da ke jihar Ogun a ranar Talata jim kadan bayan sabunta rijistarsa ta jam'iyyar APC, The Nation ta wallafa.
Mataimakin shugaban kasan yayi kira ga 'yan Najeriya da su gujewa duk wani yunkuri na tarwatsa hadin kan jama'a kuma sun yi aiki wurin tabbatar da shawo kan matsalar tsaro a kasar nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng