Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotu

Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotu

- Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin Ganduje a gaban kotu

- Malamin ya zargi gwamnatin Kano da tsaresa ba bisa ka'ida ba tare da hantararsa

- Kamar yadda lauyansa, Shuaib Kabir ya bayyana, gwamnatin ta take hakkin malamin

Abduljabar Nasir Kabara, babban malamin da gwamnatin Kano ta haramtawa wa'azi ya maka gwamnatin jihar Kotu a kan tsaresa da tayi ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin Kano ta hana Kabara wa'azi a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 a kan zarginsa da wa'azi da zai iya tada zaune tsaye, The Cable ta wallafa.

A ranar 7 ga watan Fabrairu, gwamnatin jihar ta amince da mukabala tsakanin Sheikh Kabara da sauran malaman addini a jihar.

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ya dace a sani game da sabon kakakin soji, Birgediya Janar Yerima

Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotu
Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotu. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

A wata takarda da aka mika gaban babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Laraba, Kabara ya ce abinda gwamnatin jihar Kano tayi masa yayi karantsaye ga hakkinsa na dan Adam da kuma addini.

Kabara na bukatar kotun ta umarci gwamnatin jihar, kwamishinan 'yan sandan Kano da sauran jami'an tsaro da su gujewa musgunawa, hantara da duk wata takura da suke masa.

A yayin zantawa da manema labarai bayan shigar da karar, Shuaib Kabir, lauya mai wakiltar Kabara ya zargi gwamnatin jihar da yankarwa wanda yake karewa hukunci ba tare da sauraroronsa ba.

"Cigaba da tsare shi tare da mamaye gidansa da jami'an gwamnatin jihar suka yi yayi karantsaye ga hakkinssa na dan Adam," lauyan yace.

KU KARANTA: Bidiyon kasaitattun motoci 6 da mawaki Peter Okoye ya mallaka sun gigita masoyansa

A wani labari na daban, EFCC ta gurfanar da Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama bisa zargin wawurar kudaden al'umma. An daga zaman da za a yi da ita ranar Talata saboda tsohuwar ministan bata nan.

Yanzu haka Uduah sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta arewa, kuma ana zargin ta da wasu mutane 8 a wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CR/316/20.

Hukumar tana zargin Oduah da kwasar kudin gwamnati lokacin tana minista, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel