Mai gidan haya ya lakadawa 'yar haya mugun duka, ta maka shi a gaban kotu

Mai gidan haya ya lakadawa 'yar haya mugun duka, ta maka shi a gaban kotu

- 'Yar haya ta maka mai gidan haya a gaban kotu bayan ya nada mata mugun duka

- Mai gabatar da kara ya sanar da cewa Mufutau ya yi hayar 'yan daba inda suka zane Ruth

- An gano cewa ya bata notis ta tashi mishi daga gidan shi ne amma ta ki tashi

Wani mai gidan haya mai suna Mufutau Ojomu a ranar Laraba ya bayyana a gaban wata kotun majistare da ke Ogudu a jihar Legas a kan zarginsa da ake da yi wa 'yar haya mugun duka bayan ya bata notis.

'Yan sandan suna zargin Ojomu da laifin hada kai wurin aikata laifi da cin zarafi, Vanguard ta wallafa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Dojour Perezi, ya sanar da kotu cewa mai kare kan shi ya aikata laifin a ranar 27 ga watan Disamban 2020 a layin Yisa Omotunde da ke yankin Alapere a jihar Legas.

KU KARANTA: Mata karkatar da hankali suke yi, Lauyan da yayi soyayya da mata fiye da 100

Mai gidan haya ya lakadawa 'yar haya mugun duka, ta maka shi a gaban kotu
Mai gidan haya ya lakadawa 'yar haya mugun duka, ta maka shi a gaban kotu. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Ya ce wanda ke kare kansa da wasu da har yanzu basu shiga hannu ba sun kama Ruth David sun yi mata duka saboda notis da ya bata.

Ya ce wanda ke kare kanshi ya aikata laifin da zai iya kawo karantsaye ga zaman lafiya ta hanyar hayar 'yan daba da suka zane wacce ke kara.

Ya ce wacce ke korafin bata rike da ko sisin mai gidan hayan. Wannan laifin ya ci karo da tanadin sashi na 173 da 411 na laifukan jihar Legas na 2015.

Duk da musanta laifinsa da yayi, alkali O.M Ajayi ta bada belinsa a kan N50,000 tare da dage shari'ar zuwa ranar 8 ga watan Maris.

KU KARANTA: Hukumar EFCC za ta gurfanar da Sanata Oduah a kan zargin damfara

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce nada sabbin hafsoshin tsaro da gwamnatin tarayya tayi yasa an samar da sabbin dabaru, hazaka da hanyoyin yakar ta'addanci, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Najerya.

Osinbajo ya sanar da hakan ne a Ikenne da ke jihar Ogun a ranar Talata jim kadan bayan sabunta rijistarsa ta jam'iyyar APC, The Nation ta wallafa.

Mataimakin shugaban kasan yayi kira ga 'yan Najeriya da su gujewa duk wani yunkuri na tarwatsa hadin kan jama'a kuma sun yi aiki wurin tabbatar da shawo kan matsalar tsaro a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel