Kungiya ta yi wa Malamin addini, Gumi raddi na kamanta ‘Yan bindiga da Tsagerun N/Delta

Kungiya ta yi wa Malamin addini, Gumi raddi na kamanta ‘Yan bindiga da Tsagerun N/Delta

- Kwanaki Ahmad Mahmud Gumi ya ce ya kamata a yi wa ‘yan bindiga afuwa

- Malamin ya kamanta ‘yan bindigan Arewa da tsagerun da aka yi a Neja-Delta

- Kungiyar PADEF ta ce sam babu wani abin da ya hada wadannan gungu biyu

Kungiyar Pan Niger Delta Forum wanda aka fi sani da PANDEF, ta yi magana game da wasu kalamai da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya yi kwanaki.

An rahoto Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya na cewa ya kamata a yi wa miyagun ‘yan bindiga afuwa kamar yadda aka ba tsagerun Neja-Delta lamuni.

Mai magana da yawun bakin kungiyar Pan Niger Delta Forum na kasa, Ken Robinson, ya yi hira da jaridar Punch, inda ya kore wannan kamantawar da aka yi.

Mista Ken Robinson ya ce akwai banbamci tsakanin makiyayan da ke yawo da makamai da abin da tsagerun yankin Neja-Delta su ka rika yi a shekarun baya.

KU KARANTA: Makiyaya 4000 sun bar yankin Kudu, sun dawo Jihar Kaduna

Kakakin na PANDEF yake cewa tsagerun Neja-Delta ba su kashe mutane ko su ka yi masu ta’adi ba, sannan ba su rika dakile hanyar neman abincin Bayin Allah ba.

Robinson ya kuma kara da cewa wadannan tsageru da aka yi wa afuwa sun fito su na bore ne a kan watsi da yankinsu da gwamnatin kasar da kamfanoni su ka yi.

“Ba su kashe wadanda ba su yi laifi ba. Abin da ke faru wa a Arewa maso yamma, tsantsar barna ce, kuma ya kamata a dauki wadannan mutane a matsayin masu laifi.”

“Mu na yin tir da kamanceceniyar da Sheikh Gumi ya yi; abin mamaki ne, kuma ayi fatali da shi.”

KU KARANTA: Jiragen yakin sojojin sama sun kashe 'Yan bindiga a Kaduna

Kungiya ta yi wa Malamin addini, Gumi raddi na kamanta ‘Yan bindiga da Tsagerun N/Delta
Sheikh Ahmad Gumi da ‘Yan bindiga a Zamfara Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

A wannan hira da aka yi da shi, Ken Robinson, ya zargi gwamnati da sakaci, har ya kai Sunday Igboho ya fito, ya na ikirarin cewa zai ceci mutanen kasar Yarbawa.

A ranar Laraba, 10 ga watan Fubrairu, 2021, majalisar dattawa ta fada wa jami’an tsaro suyi amfani da jiragen yaki domin bankado ‘yan bindigan da ke jeji.

‘Yan Majalisar sun bada shawara ayi wa tsarin tsaro na kasar garambawul, su ka ce akwai bukatar a duba matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Najeriya.

Matsayar ‘yan majalisar dattawar ita ce ayi kira ga shugaban kasa ya bada umarni ga NSA da sababbin hafsun sojoji da IGP a kawo karshen halin da ake ciki a yau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel