Muhimman abubuwan da ya dace a sani game da sabon kakakin soji, Birgediya Janar Yerima

Muhimman abubuwan da ya dace a sani game da sabon kakakin soji, Birgediya Janar Yerima

- Birgediya janar Mohammed M. Yerima ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello kafin ya shiga aikin soja

- Ya zama soja a shekarar 1989, ya rike mukamai iri-iri, tun 1990 kafin mukaminsa na yanzu

- Ya ketara kasashe daban-daban kuma yana cikin kungoyoyi iri-iri a Najeriya da kasashen waje

Birgediya janar Mohammed M. Yerima ya yi digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa a jami'ar Ahmadu Bello kafin ya shiga makarantar sojoji a watan Oktoban 1989.

Ya yi ayyuka iri-iri a matsayinsa na soja. Ya rike kujerar ADC ga kwamandan TRADOC, Manjo janar Ishola William tsakanin 1990-1993; jami'in hulda da jama'a na NAOWA ga hafsin sojin kasa 1994; kakakin Division 81 na sojin Najeriya a 1995-1996; PRO na NDA a 1996-2000; kakakin sojin UNM a Sierra Leone 2000-2002; PRO ga hafsin soji 2003; mataimakin jami'in hulda da jama'a na farko ga sojin Najeriya 2008. Shugaban DI a 2009 zuwa 2013.

Shine mataimakin darektan TRADOC 2013-2017 sannan ya rike kujerar mataimakin darektan RDH kafin a dauke shi wannan matsayin.

Muhimman abubuwan da ya dace a sani game da sabon kakakin soji, Birgediya Janar Yerima
Muhimman abubuwan da ya dace a sani game da sabon kakakin soji, Birgediya Janar Yerima. Hotoo daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan Auwalun Daudawa tare da mukarrabansu suna mika makamansu tare da tuba

Birgediya janar Yerima daya yake daga cikin 'yan NIPR da kuma APRA.

Ya rike shugabancin MICEM, sannan kuma sabon kakakin sojin yana daya daga cikin sojojin SSMOP a Reach Cambridge da kuma Kofi Annan Centre, Ghana.

Ya yi karatu a Sheringham United Kingdom sannan kuma ya yi US-Embassy Funded Media tour of Africom a Studgarf, kasar Jamus.

Dan asalin karamar hukumar Bade ne, a jihar Yobe, The Nation ta tabbatar.

KU KARANTA: Ke duniya! Budurwa ta aika mahaifiyarta lahira bayan watsa mata tafasasshen ruwa

A wani labari na daban, yayin da kowanne dan siyasa yake shiri akan zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar APC ba a barta a baya ba, sai dai alamun nasara suna ta harararta don yanzu haka gwamnoni 4 na jam'iyyar PDP sun shirya tsaf akan sauya shekarsu zuwa APC.

A ranar Litinin ne aka samu labarin yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya lallaba har babban birnin tarayya, Abuja don tattaunawa da shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Wani mai fadi a ji na jam'iyyar APC ya sanar da Punch cewa gaskiya ne batun zuwan Fani-Kayode wurin shugabannin jam'iyya, duk da dai tsohon ministan bai riga ya fadi wata magana ba tukunna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
NDA