Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur

Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur

- Gwamnatin jihar Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur

- Kwamishinan ilimi na jihar, Dr Aliyu Tilde ya tabbatar da hakan a yau Laraba

- Ya ce hakan yana daga cikin kokarin gwamnan na karrama mazan jiya

Majalisar jihar Bauchi ta amince da sauya sunan jami'ar jihar Bauchi zuwa Jami'ar Sa'adu Zungur.

Dr Aliyu Tilde, kwamishinan ilimi na jihar ya sanar da cewa nan babu jimawa zai fara aikin sauyin sunan.

Kamar yadda Dr Tilde ya sanar, gwamnatin tana cigaba da gwagwarmaya tare da Saudi Arabia wurin bautawa kasar nan ta hanyar koyarwar marigayi Malam Sa'adu Zugur wanda dan asalin jihar Bauchi ne.

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ya dace a sani game da sabon kakakin soji, Birgediya Janar Yerima

Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur
Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur. Hoto daga Lawal Muazu Bauchi
Source: Facebook

Fitaccen malamin makarantan ya kasance mai ilimi, dabi'a mai kyau tare da gwagwarmayar rajin kare hakkin dan Adam.

Dan siyasa Malam Sa'adu Zungur yayi rayuwa daga 1915 zuuwa 1958 kuma ya taba rike sakataren NCNC.

Tilde yace wannan matakin yana daga cikin kokari Gwamna bala Muhammad na karrama mazan jiya wadanda suka bada gudumawarsu ga gwamnatinsa da jihar bauchi baki daya.

KU KARANTA: Bidiyon kasaitattun motoci 6 da mawaki Peter Okoye ya mallaka sun gigita masoyansa

A wani labari na daban, yayin da kowanne dan siyasa yake shiri akan zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar APC ba a barta a baya ba, sai dai alamun nasara suna ta harararta don yanzu haka gwamnoni 4 na jam'iyyar PDP sun shirya tsaf akan sauya shekarsu zuwa APC.

A ranar Litinin ne aka samu labarin yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya lallaba har babban birnin tarayya, Abuja don tattaunawa da shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Wani mai fadi a ji na jam'iyyar APC ya sanar da Punch cewa gaskiya ne batun zuwan Fani-Kayode wurin shugabannin jam'iyya, duk da dai tsohon ministan bai riga ya fadi wata magana ba tukunna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel