Ka tsaya a layinka, hadimin Buhari ga Fani-Kayode bayan ya karyata batun komawarsa APC
- Mai ba Shugaba Buhari shawara kan kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bukaci Fani-Kayode da kada ya koma APC
- Ahmad ya bayyana hakan ne jim kadan bayan tsohon ministan na jirgin sama ya ce har yanzu shi dan PDP ne
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a baya yayi ikirarin cewa Fani-Kayode ya koma APC
Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafafen yada labarai ya mayar da martani ga Femi Fani-Kayode da ya musanta batun sauya shekarsa zuwa jam'iyyar All Progressives Party (APC) mai mulki.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yayi ikirarin cewa Fani-Kayode, tsohon ministan jirgin sama ya koma APC.
Gwamna Bello ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya shahara a shafin Twitter.
Gwamnan ya yi wannan bayanin ne bayan ya sabonta katin kasancewarsa dan jam’iyyar APC a mahaifarsa da ke jihar Kogi.
KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Ni fa ban fita daga PDP ba, har yanzu ina shawara, Fani Kayode ya yi fashin baki
Sai dai, jim kadan bayan faifan bidiyon ya yadu, Fani-Kayode ya wallafa a shafinsa na Twitter, @realFFK, cewa har yanzu shi dan jam'iyyar PDP ne.
Ya ce a cikin sakon da aka wallafa a yammacin Laraba, 10 ga Fabrairu:
"Duk da cewa mun yi tarurruka a duk bangarorin jam'iyya kuma muna cikin wani lokaci na shawarar siyasa ban bar PDP ba."
Hadimin Buhari ya maida martani:
'Yan mintoci kaɗan bayan rubutun Fani-Kayode, Ahmad, hadimin Shugaba Buhari ya ba shi amsa ta Twitter, inda ya ce ya kamata ya ci gaba da kasancewa a PDP.
KU KARANTA KUMA: An damke wani mutum da ya shirya sace matarsa don yin kudi da ita
Ya wallafa a saukake:
"Don Allah ka tsaya a layinka, yallabai."
A baya mun ji cewa gwamnan jihar Kogi, kuma shugaban kwamitin jan hankalin matasa zuwa APC, Alhaji Yahaya Bello, ya tabbatar da labarin cewa tsohon ministan sufurin jirage, Femi Fani Kayode, ya sauya sheka jam'iyyar APC.
Yahaya Bello a wani taron jam'iyyar ya bayyana cewa suna janyo hankulan mutane zuwa APC ne ba tare da la'akari da irin abubuwan da suka aikata a baya ba.
Fani-Kayode ya shiga jerin jiga-jigan PDP da suka koma APC a makonnin nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng