Kuma dai: Ni fa ban fita daga PDP ba, har yanzu ina shawara, Fani Kayode ya yi fashin baki
- Fani Kayode ya karyata gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello
- Kayode ya ce har yanzu yana cikn tattaunawa amma har yanzu yana PDP
- Fani Kayode a baya dai ya rantse babu abinda zai sa shi komawa jam'iyyar APC
Tsohon ministan sufurin jirage kuma babban mai adawa da shugaba Muhammadu Buhari, Femi Fani-Kayode, ya yi watsi da kalaman gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP zuwa All Progressives Congress APC.
Fani Kayode ya ce duk da cewa ya gana da shugabannin jam'iyyar APC kuma ya na da daman sauya sheka, har yanzu bai koma APC ba.
"Duk da cewa mun tattauna kan lamarin jam'iyya kuma muna cikin lokacin yin shawara, ban fita daga PDP ba," Fani Kayodeya bayyana a shafinsa na Tuwita.
KU DUBA: Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje
KU DUBA: Femi Fani-Kayode ya sauya sheka jam'iyyar APC, Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sanar da Femi Fani Kayode, ya sauya sheka jam'iyyar APC.
Yahaya Bello a wani taron jam'iyyar ya bayyana cewa suna janyo hankulan mutane zuwa APC ne ba tare da la'akari da irin abubuwan da suka aikata a baya ba.
A farkon makon nan babban jigon na jam’iyyar PDP a kudancin Najeriya ya gana da wasu kusoshin APC, har da shugaban riko, Mala Buni.
Fani-Kayode ya ce sun yi zaman ne domin tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya da siyasa da nufin kare al'umma daga tsinduma wa cikin yakin basasa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng