Yanzu-yanzu: Femi Fani-Kayode ya sauya sheka jam'iyyar APC, Yahaya Bello

Yanzu-yanzu: Femi Fani-Kayode ya sauya sheka jam'iyyar APC, Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, kuma shugaban kwamitin jan hankalin matasa zuwa APC, Alhaji Yahaya Bello, ya tabbatar da labarin cewa tsohon ministan sufurin jirage, Femi Fani Kayode, ya sauya sheka jam'iyyar APC.

Yahaya Bello a wani taron jam'iyyar ya bayyana cewa suna janyo hankulan mutane zuwa APC ne ba tare da la'akari da irin abubuwan da suka aikata a baya ba.

Fani-Kayode ya shiga jerin jiga-jigan PDP da suka koma APC a makonnin nan.

Saurari kalaman Yahaya Bello:

DUBA NAN: Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje

A farkon makon nan babban jigon na jam’iyyar PDP a kudancin Najeriya ya gana da wasu kusoshin APC, har da shugaban riko, Mala Buni.

Fani-Kayode ya ce sun yi zaman ne domin tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya da siyasa da nufin kare al'umma daga tsinduma wa cikin yakin basasa.

FFK ya ke cewa a matsayinsu na dattawan kasar nan, idan matsala ta taso gadan-gadan, dole ne a ajiye siyasa a gefe a hada kai, domin kawo cigaban al'umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel