Hotunan wani gurgu mai kafa daya da ke aikin hako kasa ya ja hankalin jama'a, sun jinjina masa

Hotunan wani gurgu mai kafa daya da ke aikin hako kasa ya ja hankalin jama'a, sun jinjina masa

- Wani matashi ya ki bari yanayin jikin sa ya hana masa yin abubuwa

- Hotunan da aka wallafa a shafin Twitter sun nuna lokacin da mutumin mai kafa daya yake aikin hako kasa

- 'Yan Najeriya sun shiga sashen sharhi don yaba wa mutumin saboda kwazonsa duk da kalubalen da yake fuskanta

Gaskiya ne maganar da ke cewa akwai iyawa cikin nakasa. Wani saurayi ya jajirce ba tare da la’akari da nakasar da ke jikinsa ba don ya sami damar biyan bukatun kansa.

An gano saurayin wanda ba a san ko wanene ba a cikin wasu hotuna da aka wallafa a shafin Twitter dauke da kayan hako kasa, yayinda ya daura sandar kugu domin tallafawa ragowar dayan kafar nasa wanda ke da nakasa.

An gano shi yana haƙa magudanar ruwa a ƙarƙashin rana mai zafi a gefen babbar hanya mai cike da jama'a.

Hotunan wani gurgu mai kafa daya da ke aikin hako kasa ya ja hankalin jama'a, sun jinjina masa
Hotunan wani gurgu mai kafa daya da ke aikin hako kasa ya ja hankalin jama'a, sun jinjina masa Hoto: @Abdullahi_wolf
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ina nan da raina ban mutu ba – Tsohon kwamishinan yan sandan Kano, CP Muhammad Wakili

Da ya wallafa hotunan, @Abdullahi_wolf ya shawarci mabiyansa da su, "zamo masu godiya ga abin da kuke da shi."

'Yan Najeriya sun yaba da jajircewar saurayin a kan neman na kansa maimakon bara ba tare da yin komai ba. Wasu sun yi addu'a a madadinsa sannan da yawa sun koyi darasi daga wajen shi.

@maameeh_M yayi sharhi:

"Duk da haka ya zabi neman na kansa maimakon ya zauna da kwano yana jiran wasu su bashi. Allah mai dukka ya albarkaci kokarin sa ya kuma saukaka masa."

@nupekid ya ce:

"Alhamdulillahi ya Allah ban taba sanin akwai wanda ya fi ni bukata ba, na gode da dimbin ni'imomin da kayi min."

@yusuf_yuza ya yi martani:

"Alhamdulillah. Mun manta yawan ni'imomin da Allah yayi mana shi yasa muke yawan korafi."

KU KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya: Buhari ba mai yawan magana bane, ba zai iya magana a kan komai ba, fadar shugaban kasa

@Amar_M_Tukur ya ce:

"Wallahi wasu abubuwan sun zarta tunani, idan ka ga hanyar samun kudinka to ka yi godiya."

A gefe guda, wasu gungun mabarata da galibinsu mata ne, sun yiwa gidan gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar kawanya. Sun nemi kuɗi, suna cewa suna jin yunwa, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya je Babura ne, mahaifar kasarsa, don sake jaddada zamansa mamba a jam’iyyar APC a mazabarsa da ke Kofar Arewa Primary School.

Nan da nan ya shiga harabar gidansa bayan da ya sake jaddada rajistar jam'iyyarsa a garinsu, mabaratan suka kewaye gidansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng